Shugaban Masallacin Sultan Bello Kaduna Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Shugaban Masallacin Sultan Bello Kaduna Ya Rigamu Gidan Gaskiya

  • Shugaban masallacin Sultan Bello dake cikin Kaduna, Alhaji Sa'idu Kakangi ya riga mu gidan gaskiya
  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, ya halarci sallar jana'iza da a ka gudanar a harabar masallacin
  • Marigayin ya samu shaida mai kyau daga bakin mutane, cikinsu harda tsohon limamin masallacin

Shugaban kwamitin gudanarwa na masallacin sultan Bello dake Kaduna, Alhaji Sa'idu Kakangi ya rigamu gidan gaskiya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ya rasu ranar Litinin a Kaduna, kuma an gudanar da jana'izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanazar a harabar Masallacin Sultan Bello, bisa jagorancin limamin masallacin Dr. Suleiman Adam.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Kira Makarantar Ta Wayar Salula

Masallacin Sultan Bello Kaduna
Shugaban Masallacin Sultan Bello Kaduna Ya Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Manyan Mutane sun halarci jana'iza

Daga cikin sanannun mutanen da suka halarci jana'izar marigayin har da, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero.

Manyan Malamai da suka haɗa da, Shahararrren Malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukum da tsohon limamin sultan Bello, Abdulhamid Balele Wali, sun samu halartar jana'iza.

Musulunci da musulmai sun yi babban rashi

Shugaban masallacin dake kan hanyar Yahaya, Alhaji Garba Ibrahim, wanda ya halarci jana'iza, ya bayyana rasuwar Kakangi a matsayin wani babban rashi ga al'ummar musulmi.

Yace: "Mako biyu da suka gabata, marigayin ya same ni yace ya kamata mu rinƙa haɗuwa a lokaci bayan lokaci domin mu rinƙa musayar shawarwari a kan yadda za'a tafiyar da masallacin nan. Bansan cewa wannan shine ganina da shi na ƙarshe ba."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Ɗage Dokar Hana Fita da Ya Sanya a Jiharsa Tsawon Wata 2

Hakazalika, tsohon limamin masallacin, Abdulhamid Balele Wali, ya bayyana mamacin da mutumin kirki wanda yake girmama kowa kuma ya sadaukar da lokacinsa ga addinin musulunci.

Wali yayi addu'a Allah ya yafe masa dukan kura-kuransa, ya sa Aljannar fiddausi ta zamo makomarsa.

A wani labarin kuma El-Rufa'i Ya Kafa Hukumar da Zata Binciki Yajin Aikin NLC da Ayuba Waba ya Jagoranta a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta kafa hukumar da zata bincike yajin aikin da ƙungiyar ƙwadugo ta gudanar a jihar a watan Mayu.

Kakakin gwamnan jihar, Mr. Muyiwa Adekeye, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ɗauke da sa hannunsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel