Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Kuɓutar da Mai Baiwa Gwamna Shawara da Aka Sace Cikin Awanni 5

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Kuɓutar da Mai Baiwa Gwamna Shawara da Aka Sace Cikin Awanni 5

  • Rundunar yan sanda ta samu nasarar kuɓutar da mai baiwa gwamna Ayade shawara da aka sace
  • Wasu yan bindiga aƙalla goma sun sace mai baiwa gwamna Cross Rivers shawara kan noman Cocoa
  • A kwanankin baya dai Mr. Ofuka ya zargi tsohon mataimakin AIG da ɗaukar nauyin kai mishi hari

Rundunar yan sanda ta jihar Cross Rivers ta kuɓutar da mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar cikin awanni 5 bayan sace shi da safiyar Talata, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Kungiyar Ƙwadugo NLC Ta Janye Yajin Aikin da Ta Kwashe Mako 3 Tana Yi

An sace Oscar Ofuka, mai baiwa gwamna Ben Ayede shawara kan noman cocoa da misalin ƙarfe 9:30 na safe a harabar tashar watsa labarai CRBC yayin da ya halarci buɗe taron Cocoa.

Kwamishinan yan sandan jihar, Sikiru Akande, ya bayyana cewa hukumarsa ta duƙufa kan aikin kuɓutar da Ofuka, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Osca Ofuka
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Mai Baiwa Gwamna Shawara Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Awanni ƙaɗan bayan yayi wannan maganar, Akande yace:

"Mun samu nasarar kuɓutar da Oscar Ofuka, awanni kaɗan bayan an yi awon gaba da shi."

"Yan jarida sun fara zargin mu a kan lamarin, yanzun lokaci yayi da zaku yaba mana, jami'an mu sun cika aiki."

Hukumar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar kuɓutar da Ofuka ne da misalin ƙarfe 2:30 da rana, a ranar da aka sace shi.

Wata majiya ta bayyana cewa waɗanda suka yi awon gaba da Ofuka sun zo ne daga hedkwatar yan sanda dake Abuja.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba da Shanu da Dama a Jihar Katsina

Ofuka ya zargi tsohon AIGP da ɗaukar nauyin ta'addanci

Watanni biyu da duka gabata, Ofuka ya kira taron manema labarai, inda ya zargi tsohon mataimakin sufetan janar na yan sanda da ɗaukar nauyin masu hari.

Ya kuma zargi tsohon AIG ɗin da gaza baiwa mutanen da suka san darajar Cocoa filayenta.

A wani labarin kuma Bayan Ya Sallame Su, Gwamna Matawalle Ya Amince da Maida Mutum 8 Muƙamansu

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya amince da naɗin wasu masu bashi shawara ta musamman mutum 8.

Waɗanda aka naɗa ɗin suna daga cikin tsofaffin mashawartansa da ya sallama a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel