Kungiyar Ƙwadugo NLC Ta Janye Yajin Aikin da Ta Kwashe Mako 3 Tana Yi
- Ƙungiyar ƙwadugo a jihar Nasarawa ta sanar da janye yajin aikin da ta shafe makonni uku tana gudanarwa
- Ƙungiyar ta amince da wannan matakin ne bayan cimma wata yarjejeniyar fahimta da ɓangaren gwamnatin jihar
- Gwamnatin Nasarawa ta amince ta fara biyan mafi karancin albashi ga ma'aikatanta
Ƙungiyar ƙwadugo NLC, reshen jihar Nasarawa ta janye yajin aikin da ta kwashe mako uku tana yi bayan cimma matsaya da gwamnatin jihar a Lafiya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Shugaban NLC ta jihar Nasarawa, Yusuf Iya, shine ya bayyana matakin janye yajin aikin jim kaɗan bayan sanya hannu a yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).
KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba da Shanu da.Dama a Jihar Katsina
Yace ƙungiyar NLC na umartar dukkan ma'aikata a faɗin jihar su koma bakin aiki daga ranar 6 ga watan Yuli 2021, kamar yadda punch ta ruwaito.
Shugaban NLC ya yaba wa sarakunan gargajiya da manyan masu faɗa a ji bisa namijin ƙoƙarin su wajen ganin an sasanta ma'aikata sun koma bakin aiki.
Gwamnati zata yiwa ma'aikata ƙarin girma
Bayan taron, Antoni janar kuma ministan shari'a na jihar, Abdulkarin Kana, ya karanta abinda yarjejeniyar da aka amince da ita ta ƙunsa ga shugabannin NLC da kuma ɓangaren gwamnati bisa jagorancin shugaban ma'aikata, Abari Aboki.
A cewar Antoni Janar gwamnatin Nasarawa ta amince ta aiwatar da ƙarin girma a tsakanin ma'aikata wanda aka shekara 10 ba'a yi ba daga watan Agusta 2021.
Kana, yace: "Gwamnati ta amince zata biya albashin ma'aikata da ba'a biya ba tun watan Agusta 2016."
KARANTA ANAN: Bayan Ya Sallame Su, Gwamna Matawalle Ya Amince da Maida Mutum 8 Muƙamansu
Za'a fara biyan mafi ƙarancin albashi
A ɓangaren mafi ƙarancin albashi na N30,000 kuma, kwamishinan yace dukkan ɓangarorin biyu sun amince a fara aiwatar da shirin daga ma'aikatan dake mataki na 1 zuwa 7.
Yayin da zasu cigaba da tattaunawa domin cimma matsaya kan ma'aikatan dake mataki na 8 zuwa sama.
Kana, yace: "Dukka ɓangarorin biyu sun amince a fara biyan mafi ƙaranci. albashi daga ma'aikatan dake mataki na 1 zuwa na 7, yayin da sauran ma'aikatan za'a cigaba da tattaunawa a kansu."
A wani labarin kuma Bayan Taro a Lagos, Gwamnonin Kudu Sun Kafa Sharaɗi Ga Dukkan Jami'an Tsaro
Gwamnonin kudancin ƙasar nan sun bayyana cewa daga yanzun ya zama wajibi idan jami'an tsaro zasu cafke wani ɗan yankin su sanar da gwamnan jihar.
Hakanan kuma sun bayyana cewa bayan kammala mulkin shugaba Buhari, ɗan yankin su ne zai gaje shi.
Asali: Legit.ng