Jihar Legas za ta sanya dokar hana gabatar da wadanda aka kame da laifi a gaban 'yan jarida
- Majalisar dokokin jihar Legas na neman sake dokar gabatar da masu laifuka a jihar Legas
- Majalisar ta bayyana hujjojinta na sauyin, tana mai mika kudurin ga gwamnan jihar ta Legas
- A baya-bayan nan an gabatar da wata dalibar jami'ar Legas da ta kashe wani saurayinta, lamarin da ya jawo cece-kuce
Majalisar dokokin jihar Legas ta zartar da kudirin gyaran dokar Kundin Laifuka ta 2015 a jihar, wacce ke neman hana ‘yan sanda gabatar da wadanda ake zargi a gaban 'yan jarida, The Cable ta ruwaito.
Kudirin gyaran, mai taken: ‘Bill of Administration of Criminal Justice (Amendment) Bill, 2021’, an mika shi ne a ranar Litinin a yayin zaman da mataimakin kakakin majalisar, Wasiu Eshilokun-Sanni ya jagoranta.
KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Bayan mako guda, gwamna Matawalle ya bayyana dalilinsa na komawa APC
A dokar gyaran, sashi na 9 (a) ya ce:
"Tun daga lokacin wannan dokar zata fara aiki, 'yan sanda za su daina gabatar da duk wani wanda ake zargi a gaban manema labarai".
Wannan ya nuna cewa a karkashin dokar shari'ar manyan laifuka ta jihar Legas, zai zama ya saba doka ga jami'an 'yan sanda su gabatar da wadanda ake zargi a gaban manema labarai a jihar.
A cikin 'yan kwanakin nan, masu ruwa da tsaki a tsarin shari'ar manyan laifuka sun nuna damuwarsu kan gabatarwar da jami'an 'yan sanda ke yi wa wadanda ake zargi -
Sun buga misali da na baya-bayan nan, lokacin da aka gabatar da Chidinma Ojukwu, dalibar Jami'ar Legas, kan zargin kisan Usifo Ataga shugaban Super TV.
Kwaskwarimar dokar na kushe da tarin sauye-sauye, wadanda ake sa ran za su shafi aikin 'yan sanda kai tsaye.
Mataimakin kakakin ya kuma umurci Olalekan Onafeko, mukaddashin magatakarda na majalisar da ya gabatar da kudirin zuwa ga Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas don ya amince da kwaskwarimar.
Gwamnonin Kudu sun ce basu amince a sake kame wani a yankinsu ba sai da izininsu
Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, Gwamnonin kuduncin Najeriya sun yi shawaricewa, hukumonin tsaro dake aiwatar da ayyukansu a yankin dole ne su sanar da gwamna kafin kame ko wani aiki.
A wani taro, Kungiyar Gwamnonin Yankin Kudu (SGF), a ranar Litinin, ta dage cewa duk wata hukumar tsaro da ke gudanar da wani aiki a kowane yanki na Kudu dole ne ta karbi izini daga gwamnan jiha kafin ta kame wani a yankin saboda gwamna shi ne babban jami'in tsaro a jiha.
Wani yankin sanarwar ya ce:
"An yanke shawarar cewa idan har ta kowane dalili hukumomin tsaro na bukatar gudanar da aiki a kowace jiha, dole ne a sanar da Babban Jami'in Tsaron Jihar yadda ya kamata.
"Kungiyar ta nuna rashin jin dadi game da son kai a hukunce-hukuncen Shari'a kuma ta yanke shawara cewa kame ya kamata a yi shi bisa tsarin doka da hakkin dan adam na asali."
KARANTA WANNAN: Lamari ya yi zafi: Sarkin Yarbawa ya shawarci Sunday Igboho ya mika kansa ga DSS
An Kame 'Yan Gangamin Kafa Kasar Yarbawa 47 Dauke da Layu, Zasu Bayyana a Kotu Gobe
A wani labarin, Jihar Legas - A rahoton da Legit.ng Hausa ta samo, rundunar 'yan sanda ta jihar ta cafke wasu daga cikin masu gangamin kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa a yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a jiya Asabar a cikin jihar.
Bayan tabbatar da kamun, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Hakeem Odumosu ya gabatar da wasu mutane 47 da aka kama a wurin zanga-zangar ta nuna goyon baya ga kafa haramtacciyar kasar Yarbawa.
An gabatar da hotuna, mazuban abinci, layu, da sauransu a matsayin abubuwan da aka kame yayin zanga-zangar.
Asali: Legit.ng