Ba Zan Taɓa Dena Sukar Shugaba Buhari Ba, Gwamna Samuel Ortom
- Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya ce ba zai taba dena sukar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba
- Gwamna Ortom ya ce yana sukar gwamnatin tarayyar ne domin hakan zai sa kada ta kauce hanya
- Ortom ya kuma kara da cewa sukar da ya ke yi wa gwamnatin mai amfani ne ba wai na kiyayya ko da mugun nufi ba
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya ce zai cigaba da sukar fadar shugaban kasa domin hakan ne zai sa ta rika yin abin da ya dace, The Sun ta ruwaito.
Ortom, wanda ya yi wannan furucin bayan duba wasu ayyuka da gwamnatinsa ke yi a Makurdi, babban birnin jihar Benue kamar yadda Daily Sun ta ruwaito.
DUBA WANNAN: El-Rufai: Dalilan da yasa bai zai dace a kwatanta Nnamdi Kanu da Sheƙau ba
Gwamnan ya ce sukar da ya ke yi na gyara ne ba batanci ba yana mai cewa;
"Kuma ba zan dena ba. Idan fadar shugaban kasa ta yi wani abu mai kyau, zan yaba mata amma idan ta yi ba dai-dai ba, zan soke ta. Suka ta mai amfani ne ba na batanci bane.
"Ya kamata mutane su gane banbancin. A matsayi na na kirista, na yi imani da koyarwar addinin kirista da ya ce a rika yi wa shugabanni addu'a ko da sun yi ba dai-dai ba; Allah na iya sauya halayensu su bamu abin da muke bukata.
"Abin da muke nema shine shugabanci na gari. Abin da muke so shine adalci, dai-daito, da kyautatawa kowa, shikenan. A yanayin da wadanda ake zalunta ba su iya magana, ina magana a madadinsu. Ina tare da su har sai anyi abin da ya dace."
Da aka masa tambaya game da kalaman da kwamishinansa ya furta na gayyatar Fulani su zo suyi kasuwanci a Benue, Ortom ya ce an jirkita maganan kwamishinansa ne domin tunda farko bai hana wadanda za su yi sana'a yin abinsu a Benue ba, masu kisa ne baya maraba da su.
Har ila yau, gwamnan na Benue ya ce bashi da niyyar komawa jam'iyyar APC mai mulki kamar yadda wasu gwamnonin PDP suka yi yana mai cewa APC bata tsinana komai ba don haka babu dalilin ya shiga jam'iyyar.
An kama wasu sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' a wata Coci a Abuja
A wani labarin daban, wasu masu zanga zanga da suka sanya riga dauke da rubutun 'Buhari-must-go' don zuwa Cocin Dunamis Gospel mai hedikwata Lugbe, Abuja, sun shiga hannu kuma rahotanni sun ce tuni aka mika su ga rundunar tsaro ta farin kaya DSS, News Wire ta ruwaito.
Dan gwagwarmayar siyasa kuma mamallakin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya ruwaito,
"Jami'an tsaro a Cocin Dunamis sun kama yan gwagwarmaya sanya da rigar #BuhariMustGo lokacin da za su shiga Cocin don gudanar da ibada, daga baya kuma jami'an tsaron Cocin suka mika su ga hukumar DSS, wanda suke azabtar dasu a halin yanzu.
"Ina tunanin Pastor Dr Paul Eneche shima wa'azi yake akan adalci! An tafi da yan gwagwamayar su biyar a mota kirar Hilux da kuma manyan babura. Abun kunya a dakin ubangiji."
Asali: Legit.ng