El-Rufai: Dalilan da yasa bai zai dace a kwatanta Nnamdi Kanu da Sheƙau ba

El-Rufai: Dalilan da yasa bai zai dace a kwatanta Nnamdi Kanu da Sheƙau ba

  • Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce kwakwata bai dace a kwatanta Nnamdi Kanu da Shekau ba ko yan bindiga
  • Gwamnan na Kaduna ya ce yan bindiga ba su da shugaba guda daya makamancin Kanu kuma ba nema suke yi raba kasa ba
  • El-Rufai ya ce yan bindigan ba su da wata takamamen wurin da suke zaune ko kafafen watsa labarai da suke isar da sakonni ga mabiyansu

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce yan bindiga ko Boko Haram ba dai-dai suke da Nnamdi Kanu ba shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Daily Trust ta ruwaito.

Bayan kama Nnamdi Kanu, wasu masu sukar gwamnatin tarayya sunyi zargin cewa gwamnatin Buhari na sakwa-sakwa da batun 'yan bindiga.

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Kaduna Mallam Nasir El-Rufai. Hoto: Gwamnatin Kaduna
Asali: Facebook

Sun kuma nemi gwamnatin tarayyar ta yi gaggawar kama 'yan bindigan.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kama ɗan aiken ISWAP da aka tura Legas ya siyo wa 'yan ta'adda kaya

Sai dai a wata hira da ya yi da BBC Pidgin, El-Rufai ya ce ba dai-dai bane a rika kwatanta yan bindiga da Kanu.

Dalilan da yasa bai kamata a kwatanta yan bindiga da Nnamdi Kanu ba

Da aka masa tambaya cewa ko ya dace a kama yan bindiga cikin ga gaggawa kamar Kanu, El-Rufai ya ce:

"Aa! Aa! Aa! Mutane na kwatanta lemu ne da tuffa."
"Nnamdu Kanu ne shugaban IPOB, kungiyar da aka haramta. An san shi, yana magana da mutane sosai kuma kowa ya san inda ya ke.
"Idan aka dauki Boko Haram a misali. Shekau ya kasance yana buya tsawon shekaru 10 kuma sojoji suna yakarsa.
"Ba wai kama Shekau yana zaune a wuri daya bane a Saudiyya, yana rubutu a twitter yana cewa a raba Nigeria ko yana cewa Boko Haram ta tafi ta kashe Helen ko Nasir El-Rufai.

KU KARANTA: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

"Nnamdi Kanu yana wuri daya ne yayin da Shekau yakin sonkoro ya ke yi. Har yanzu akwai yan bindiga amma gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba."
"Idan ka duba yan bindiga, ba su da wani takamammen shugaba. Wanene shugaban yan bindiga? Wanene ke matsayin Nnamdi Kanu a cikin yan bindiga?
"Yan bindiga bata gari ne kawai masu zaman kansu. Kasuwanci ne a wurinsu. Ba maganan raba kasa ne ke gabansu ba.
"Ina kallubalantar kowa ya fada min wanene shugaban yan bindiga wanda za a iya kwatanta shi da matsayin Kanu."

El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ya yi matuƙar murnar kama Nnamdi Kanu

A wani labarin daban, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana farin cikinsa game da kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), News Wire ta ruwaito.

Ministan shari'a kuma Attoni Janar na kasa, Abubakar Malami (SAN), a ranar Talata, ya sanar yayin taron manema labarai cewa an kama Kanu tun a ranar Lahadi.

Da ya ke tsokaci a kan kamen lokacin da aka yi hira da shi a BBC Pidgin a ranar Juma'a, El-Rufai ya ce ya yi murna da kama Kanu saboda ya tsere bayan bashi beli sannan yana kirar Nigeria 'Zoo' wato gidan namun daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel