Karin Bayani: Gwamnonin Kudu sun ce basu amince a sake kame wani a yankinsu ba sai da izininsu
- Gwamnonin yankin kudancin Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu da yadda jami'an tsaro ke ayyukansu a yankin
- Sun bayyana cewa, daga yanzu dole ne jami'an tsaro su nemi izini daga gwamnan jiha kafin su kame wani a yankin
- Hakazalika sun dage kan cewa, dole ne shugabancin Najeriya a zaben 2023 ya dawo yankin kudancin Najeriya
Gwamnonin kuduncin Najeriya sun yi shawaricewa, hukumonin tsaro dake aiwatar da ayyukansu a yankin dole ne su sanar da gwamna kafin kame ko wani aiki.
A wani taro, Kungiyar Gwamnonin Yankin Kudu (SGF), a ranar Litinin, ta dage cewa duk wata hukumar tsaro da ke gudanar da wani aiki a kowane yanki na Kudu dole ne ta karbi izini daga gwamnan jiha kafin ta kame wani a yankin saboda gwamna shi ne babban jami'in tsaro a jiha.
KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Wasu daga cikin daliban Baptist sama da 100 da aka sace sun kubuta
Wani yankin sanarwar ya ce:
"An yanke shawarar cewa idan har ta kowane dalili hukumomin tsaro na bukatar gudanar da aiki a kowace jiha, dole ne a sanar da Babban Jami'in Tsaron Jihar yadda ya kamata.
Kungiyar ta nuna rashin jin dadi game da son kai a hukunce-hukuncen Shari'a kuma ta yanke shawara cewa kame ya kamata a yi shi bisa tsarin doka da hakkin dan adam na asali."
Gwamnonin Kudu sun dage sai dai a samu shugaban kasa a yankinsu a zaben 2023
Hakazalika, Legit.ng Hausa ta tattaro kungiyar ta dage kan na cewa, ya kamata Shugaban kasar Najeriya na gaba ya fito daga yankin Kudu.
Sanarwar ta ce:
"Kungiyar ta sake jaddada kudirinta na siyasa na daidaito da adalci kuma gaba daya an amince cewa shugabancin Najeriya zai kasance karba-karba tsakanin yankunan Kudanci da Arewacin Najeriya kuma an yanke shawara cewa shugaban Najeriya na gaba ya fito daga Yankin Kudancin."
KARANTA WANNAN: 'Yan Sanda Sun Ceto Jariri Dan Wata Goma da 'Yar Aikin Gida Ta Sace
A wani labarin na daban, Rahotanni da Legit.ng Hausa ke samu sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasar Najeriya, Obasanjo na aiki kan kirkirar wata sabuwar jam'iyyar da za ta dauki mambobin jam'iyyar adawa ta PDP da mai ci ta APC wadanda ke cikin damuwa gabanin zaben 2023 mai zuwa.
Wata majiya mai karfi ta fadawa jaridar Vanguard cewa Obasanjo ya gamsu cewa akwai yiwuwar manyan jam'iyyun siyasar biyu su shiga cikin rikice-rikice na doka da siyasa wanda zai bar su cikin mummunan hali, watakila ya kai su rasa jagorancin kasar a zaben na 2023.
Majiyar ta ce duk da cewa tsohon Shugaban kasar ya yayyaga katin zama dan jam’iyyar PDP tare da yin murabus daga siyasa, amma har yanzu yana himmatuwa wajen hada kan ’yan Najeriya don yin tasiri kan fitowar shugaban kasa na gaba, gwamnoni da sauran shugabanni.
Asali: Legit.ng