Masari ya haramta bara a Katsina, ya yi wa islamiyoyi gargadi
Gwamnatin Jihar Katsina ta hana barace-barace a fadin jihar kana ta yi wa makarantun allo da na islamiyya da ke jihar kashedin cewa har yanzu ba a basu damar cigaba da karatu ba.
Gwamnatin ta ce sassauta dokar kulle a jihar bai bayar da damar bude makarantu domin cigaba da karatu a cikinsu ba.
Sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Inuwa a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya ce an cimma zartar da wadannan matakan ne bayan bita kan halin da jihar ke ciki yayin wani taro.
Taron ya samu hallarcin wakilan gwamnati, hukumomin tsaro, malaman addinin musulunci, shugabannin addini da mambobin kwamitin kar ta kwana na yaki da coronavirus na jihar.
DUBA WANNAN: An kama mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki a Borno
An gudanar da taron ne a Janar Muhammadu Buhari House kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce duk wanda aka kama yana bara zai fuskanci hukunci sannan malaminsa ko iyayensa suma za a hukunta su.
A cewarsa, gwamnatin ta lura cewa wasu masu makarantun islamiyya da na allo sun bude makarantunsu bayan sassautar dokar kulle na COVID-19 da aka yi a jihar.
Bayan bayar da umurnin rufe makarantun, gwamnan jihar ya bawa hukumomin tsaro umurnin kama duk wani wanda aka samu yana saba dokar tare da hukunta shi.
An kuma tunatar da mutane da su cigaba da bin shawarwarin kwararrun maaikatan lafiya kamar saka takunkumi, bayar da tazara, wanke hannu lokaci zuwa lokaci da sabulu ko amfani da sanitizer.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng