Da Duminsa: Bayan mako guda, gwamna Matawalle ya bayyana dalilinsa na komawa APC

Da Duminsa: Bayan mako guda, gwamna Matawalle ya bayyana dalilinsa na komawa APC

  • Bayan yada cece-kuce daban-dagan kan dalilan da yasa Matawalle ya koma APC, karshe ya yi magana
  • Ya bayyana dalilansa na koma jam'iyyar APC mai mulki don ci gaban jama'ar jiharsa ta Zamfara
  • Gwamnan ya bayyana yadda ya mori abubuwan alheri daga shugaba Buhari duk da a da yana PDP

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a ranar Litinin, ya ce ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki ne domin karfafa hadin kan siyasa a jiharsa, Premium Times ta ruwaito.

Mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Yusuf Idris, wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, ya kuma karyata rahotannin da aka yada ta kafafen yada labarai cewa an tilasta wa gwamnan shiga APC ne don dakatar da kashe-kashe a jihar.

KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Obasanjo ya magantu kan zargin kafa jam'iyya, ya ce ba ruwansa da siyasa

Yusuf Idris ya ce:

"Sanannen abu ne cewa Gwamna Matawalle na daya daga cikin shugabanni a kasar nan dake magana da hikima a kan dukkan al'amura, kuma ya koma APC ne domin karfafa hadin kan siyasa a jihar da nufin kawo ci gaba ga mutanensa."
Da Duminsa: Bayan kwanaki, Matawalle ya bayyana dalilan da suka sa ya koma jam'iyyar APC
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun gwamnan ya kara da cewa sauya shekar ya kasance ne saboda:

"Manyan alherai da shi (gwamnan) ke mora daga Shugaba Muhammadu Buhari da kuma babban jagoran APC a kan dukkan al'amuran da suka shafi jihar."

Mista Idris ya ce Shugaba Buhari da gwamnonin APC sun tausaya wa mutanen jihar a lokutan da suka shiga wahala, ya kara da cewa wadannan sun karfafa wa gwamnan gwiwa don ba da tukuici ga nuna damuwa da girmamawar da aka ba su.

“Manufar gwamnan na shiga jam’iyya mai mulki ba wani abu bane face hakan. Duk wani rahoton da aka gabatar akwai rudu a cikinsa da kuma ayyukan wadanda suka yi kaurin suna wajen adawa da sauya sheka zuwa APC da Gwamna Matawalle ya yi.”

Mista Matawalle ya koma APC ne a makon da ya gabata. Ya shiga jam’iyya mai mulki tare da dukkan ‘yan majalisun tarayya da na jihar a Zamfara amma mataimakinsa, Mahdi Aliyu, da wani dan majalisar jihar, Kabiru Yahaya, sun zabi ci gaba da kasancewa a PDP.

Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP zuwa Jam'iyya mai mulki ta APC.

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da mai taikawa shugaban ƙasa Buhari ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, yayi a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Facebook.

Bashir Ahmad, ya rubuta a shafinsa cewa:

"Zamfara ta dawo gida, lale marhabun gwamna Matawalle."

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Buhari za ta samar wa ma'aikatan kashe gobara bindiga, ta fadi dalili

Bayan Zarge-Zargen PDP Cewa APC Na Shirya Manakisa, APC Ta Mayar da Martani

A wani labarin, Jam'iyyar APC mai mulki ta yi watsi da zarge-zargen da ke danganta ficewar wasu gwamnoni daga jam'iyyar PDP da kitsa wani makircin magudi a babban zaben shekarar 2023.

PDP ta sake fuskantar wani mummunan rauni a ranar Talata saboda sauya shekar da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi zuwa APC, Premium Times ta ruwaito.

A martanin da ya mayar, Shugaban PDP na Kasa, Uche Secondus, ya ce ficewar ta gwamna Matawalle ko ta gwamnonin da suka gabata bai dami jam'iyyar ba. Ya zargi jam’iyya mai mulki da jawo gwamnoni don yin magudin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel