An Kame 'Yan Gangamin Kafa Kasar Yarbawa 47 Dauke da Layu, Zasu Bayyana a Kotu Gobe

An Kame 'Yan Gangamin Kafa Kasar Yarbawa 47 Dauke da Layu, Zasu Bayyana a Kotu Gobe

  • Runduar 'yan sandan jihar Legas za su gurfanar da masu gangamin kafa kasar Yarbawa mutum 47
  • Rahoton da Legit.ng ta samo ya bayyana hotunan ababen da aka kame tare da mutanen
  • Za a gurfanar dasu a gaban kotu gobe Litinin don tabbatar da adalcin abubuwan da suka aikata

Jihar Legas - A rahoton da Legit.ng Hausa ta samo, rundunar 'yan sanda ta jihar ta cafke wasu daga cikin masu gangamin kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa a yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a jiya Asabar a cikin jihar.

Bayan tabbatar da kamun, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Hakeem Odumosu ya gabatar da wasu mutane 47 da aka kama a wurin zanga-zangar ta nuna goyon baya ga kafa haramtacciyar kasar Yarbawa.

An gabatar da hotuna, mazuban abinci, layu, da sauransu a matsayin abubuwan da aka kame yayin zanga-zangar.

KARANTA WANNAN: An Cafke Wasu 'Yan Bindiga Bayan Karbar Kudin Fansa Da Kashe Wanda Suka Sace

An Kame Masu Gangamin Kafa Kasar Yarbawa 47 Dauke Da Layu, Zasu Bayyana a Kotu
Taswirar jihar Legas | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yanzu haka an dauke su daga birnin Ikeja zuwa Panti dake Yaba a jihar Lagos, in ji wani shafin Facebook mai suna Ilana Omo Oodua TV na yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya.

A cewar rahoton kafar, ta samu labarin cewa masu gangamin da ba su aikata wani laifi ba face zanga-zanga, za a gurfanar da su a kotu gobe Litinin a Yaba.

Hakazalika rahoton ya ce ana gayyatar dukkan lauyoyin Yarbawa, 'yan gwagwarmaya da 'yan jarida da su zo sauraran zaman kotun cikin lumana da tsari a gobe.

Kalli hotunan:

An Kame Masu Gangamin Kafa Kasar Yarbawa, Za a Gurfanar Dasu a Kotu
Masu gangamin kafa kasar Yarbawa | Hoto: Ilana Omo Oodua TV
Asali: Facebook

An Kame Masu Gangamin Kafa Kasar Yarbawa, Za a Gurfanar Dasu a Kotu
Masu gangamin kafa kasar Yarbawa | Hoto: Ilana Omo Oodua TV
Asali: Facebook

An Kame Masu Gangamin Kafa Kasar Yarbawa, Za a Gurfanar Dasu a Kotu
Masu gangamin kafa kasar Yarbawa | Hoto: Ilana Omo Oodua TV
Asali: Facebook

Rikici ya rincabe a Legas bayan masu son kafa kasar Yarabawa sun bijirewa 'yan sanda

Rikici ya rincabe a yankin Ojota na jihar Legas yayin da masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa suka bijirewa umarnin 'yan sanda suka fara zanga-zanga.

Duk da 'yan sanda da sojoji sun mamaye wurin zanga-zangar a sa'o'in farko na yau Asabar, masu zanga-zangar daga bisani sun tsinkayi wurin, Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma jami'an tsaro dauke da bindigogi sun yi kokarin hana su zanga-zangar.

Hakan ya janyo barazana ga zaman lafiyan yankin yayin da jama'a suka fara gudun ceton rai kuma 'yan sanda suka dinga watsa barkonon tsohuwa.

'Yan kasuwa masu tarin yawa sun rufe shagunansu domin gudun su fada lamarin kuma su tafka muguwar asara. Kamar yadda Daily Trust ta gani, wasu 'yan sanda sun fara kama wasu daga cikin masu zang-zangar.

KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Tankar Gas Ta Fadi a Kasuwa, Ta Yi Kaca-Kaca da Mutane 10

Bayan Kame Nnamdi Kanu, Yarbawa Sun Gargadi Sunday Igboho Kan Fafutukar Ballewa

A wani labarin, An aika sako ga mai rajin ballewar Yarbawa daga Najeriya, Sunday Adeyemo Igboho da aka fi sani da Sunday Igboho.

Sakon wanda Kungiyar Walwalar Yarbawa (YWG) ce ta aiko dashi, in ji jaridar Daily Trust, shi ne: - ya dauki darasi daga abinda ya faru da Nnamdi Kanu.

Wannan na zuwa ne yayin da Igboho ke dagewa kan cewa babu gudu babu ja da baya a ranar Asabar, 3 ga watan Yuli cewa sai ya gudanar da taron Yarbawa a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel