Barazanar Tsaro a Abuja, FCTA Ta Rushe Gine-Gine Sama da 400 a Kan Hanyar Filin Jirgi

Barazanar Tsaro a Abuja, FCTA Ta Rushe Gine-Gine Sama da 400 a Kan Hanyar Filin Jirgi

  • FCTA ta rushe wasu gine-gine da runfuna da aka kafa sama da 400 a kan hanyar filin jirgin Nnamdi Azikwe
  • Tace ta ɗauki wannan matakin ne domin kare al'ummar birnin tarayya tare da dukiyoyinsu
  • Daracktan tsaro na FCTA, yace ba zasu zauna su zuba ido wasu bara gurbi su mamaye birnin Abuja ba

Hukumar dake kula da babban birnin tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wasu gine-gine sama da 400 a kan hanyar filin jirgin Nnamdi Azikwe saboda suna barazana ga tsaro, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Ƙwadugo NLC

Shugaban kwamitin tsaftace birnin Abuja, Ikharo Attah, wanda ya jagoranci aikin ya bayyana cewa an yi haka ne domin tabbatar da tsaro ga mutane da dukiyoyinsu.

Premium times ta ruwaito cewa aikin rusau ɗin ya shafi Lugbe-Across, Lugbe-Berger, wurin wankin mota da kuma Lugbe Zone 5, ya shafe kimanin awanni 8 ana yinsa.

FCTA Ta Rushe Gine-Gine Sama da 400 a Kan Hanyar Filin Jirgi
Barazanar Tsaro a Abuja, FCTA Ta Rushe Gine-Gine Sama da 400 a Kan Hanyar Filin Jirgi Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Hakanan kuma an gudanar da rushe gine-ginen ne tare da tsattsauran tsaro daga jami'an tsaro saboda abinda ka iya zuwa ya dawo.

Jami'an tsaron sun haɗa da yan sanda, jami'an NSCDC, Sojojin ƙasa, jami'an hukumar shige da fice, sojojin sama, da sauransu.

Mun samu rahoton ana takurawa mutane

Mr. Attah yace FCTA ta samu rahoton cewa wasu gine-gine da runfuna da aka kafa ba bisa ƙa'ida ba suna takura wa jama'a a kan hanyar jirgi duk kuwa da rusau ɗa aka yi lokuta da dama a yankin.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba da Ɗalibai da dama a Kaduna

Yace: "Makon da ya gabata, munzo nan mun yi rusau, amma mutane sun sake zuwa sun kafa wurin sana'ar su, yau ma mun sake rushe su."

Daraktan sashin tsaro na hukumar FCTA, Adamu Gwary, yace ba zai yuwu su zuba ido suna kallo wasu bata gari su mamaye birnin Abuja ba.

A wani labarin kuma Gwamna Masari Ya Rushe wasu Gine-Gine a Jiharsa, Yace Sun Saɓa Wa Doka

Hukumar tsara birane da karkara ta jihar Katsina , (URPB) ta rushe wasu gine-gine da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba a yankin Morawa, ƙaramar hukumar Ɓatagarawa.

Kakakin ma'aikatar ƙasa ta jihar, Alhaji Yakubu Lawal, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi a Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel