Da Duminsa: Wasu daga cikin daliban Baptist sama da 100 da aka sace sun kubuta
- Hukumomin tsaro sun samu nasarar ceto dalibai da daga hannun 'yan bindiga a jihar Kaduna
- Sun samu nasarar ceto akalla dalibai sama da 20 tare da wata malamar makaranta da aka sace
- Rahotanni sun ce, an kai hari makarantar Bethel Baptist dake jihar Kaduna da safiyar ranar Litinin
Hukumar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ce an samu nasarar ceto 27 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su daga makarantar Bethel Baptist da ke Maraban Rido, wani yannki a karamar hukumar Chikun da ke jihar, Channels Tv ta ruwaito.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna Muhammed Jalige ya ce, an samu nasarar kubutar da dalibai 26 da kuma wata mata malama, bayan da hadin gwiwar jami’an 'yan sanda na Najeriya, Sojoji da na Sojojin Ruwa, suka fatattaki ‘yan bindigan bayan an sanar da su faruwar harin.
KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Bayan mako guda, gwamna Matawalle ya bayyana dalilinsa na komawa APC
Wasu shaidu sun ce akalla dalibai 100 ‘yan bindigan suka sace a makarantar Bethel Baptist amma har yanzu 'yan sanda da hukumomin makarantar ba su bayar da wani adadi na hukuma ba.
Kakakin 'yan sandan, wanda ya bayyana lokacin harin da karfe 1:43 na safe, ya ce ana kokarin tabbatar da kubutar da dukkan wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma dawo da su lami lafiya.
Ya ce:
“Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto don ganin an dawo da duk wadanda abin ya shafa lafiya"
Rundunar da take magana ta karfafa gwiwar iyaye kan cewa kada su karaya da ayyukan ‘yan bindiga a jihar daga kai 'ya'yansu zuwa makaranta.
An bayyana cewa maharan sun haura shinge ne domin kutsawa cikin makarantar da safiyar ranar Litinin.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Buhari za ta samar wa ma'aikatan kashe gobara bindiga, ta fadi dalili
A wani rahoton jaridar Punch, Emmanuel Paul, wani malami a makarantar ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP adadin daliban da aka sace, ya ce:
“Masu garkuwan sun tafi da dalibai 140, dalibai 25 ne suka tsere. Har yanzu ba mu san inda aka kai daliban ba.”
'Yan Sanda Sun Ceto Jariri Dan Wata Goma da 'Yar Aikin Gida Ta Sace
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta yi nasarar ceto wani jariri dan watanni 10 da ake zargin wata budurwa 'yar aikin gida ta sace bayan awanni 48 da bayyana jaririn ya bata.
Mahaifiyar yaron, Fauziya Aminu Tukur, ta tabbatar da labarin kubutar yaron ga manema labarai.
An ruwaito yadda mahaifiyar ta sanar a ranar Juma’a cewa, bayan ta dawo daga makaranta sai ta ga cewa ’yar aikin gidanta Hauwa, ta dauki jaririn zuwa wani wurin da ba a sani ba. Daily Trust ta tattaro cewa ’yan sanda sun hada yaron da mahaifiyarsa.
Asali: Legit.ng