'Yan Sanda Sun Ceto Jariri Dan Wata Goma da 'Yar Aikin Gida Ta Sace

'Yan Sanda Sun Ceto Jariri Dan Wata Goma da 'Yar Aikin Gida Ta Sace

  • 'Yan sanda sun tabbatar da cafke wata 'yar aiki da laifin sace wani jariri dan wata 10 a jihar Kaduna
  • An ceto yaron tare da mika shi ga mahaifiyarsa yayin da aka tsare 'yar aikin tare da yi mata tambayoyi
  • Mahaifiyar yaron ta shawarci iyaye da su kula wajen daukar 'yar aiki ta gari don kaucewa fitina

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta yi nasarar ceto wani jariri dan watanni 10 da ake zargin wata budurwa 'yar aikin gida ta sace bayan awanni 48 da bayyana jaririn ya bata.

Mahaifiyar yaron, Fauziya Aminu Tukur, ta tabbatar da labarin kubutar yaron ga manema labarai.

An ruwaito yadda mahaifiyar ta sanar a ranar Juma’a cewa, bayan ta dawo daga makaranta sai ta ga cewa ’yar aikin gidanta Hauwa, ta dauki jaririn zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Daily Trust ta tattaro cewa ’yan sanda sun hada yaron da mahaifiyarsa.

KARANTA WANNAN: Abu Kamar Wasa: Yadda Yara 10 Suka Bakunci Lahira Bayan Cin Tuwon Dawa

'Yan Sanda Sun Ceto Jariri Dan Wata Goma da 'Yar Aikin Gida Ta Sace
'Yan sandan Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ba a samu cikakkun bayanai game da yadda aka kama wacce ake zargin ba, amma an ce tana hannun ‘yan sanda.

Fauziya ta ce:

“‘Yan sanda sun kawo min dana a daren jiya sannan suka tafi tare da wacce ake zargin.
"Ban san yadda da inda suka kama ta ba."

Ta nuna godiya ga Allah da ya dawo mata da danta cikin koshin lafiya yayin da ta gargadi iyaye da su kiyaye yayin daukar 'yan aikin gida.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Jalige Mohammed, ya tabbatar da dawowar jaririn, yana mai cewa ana yi wa 'yar aikin tambayoyi.

Ya ce wani direban motar bas ne ya kawo wanda ake zargin zuwa ofishin ‘yan sanda na Unguwar Sunusi bayan ya gano ta da jaririn da da alamu ba nata bane a tashar motar Kawo.

KARANTA WANNAN: An Kame 'Yan Gangamin Kafa Kasar Yarbawa 47 Dauke da Layu, Zasu Bayyana a Kotu Gobe

'Yan Sanda Sun Shiga Shagali Bayan Da ’Yar Sanda Ta Haifi Jarirai ’Yan Uku

A wani labarin, Wata ‘yar sanda da ke aiki a rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun, Bolaji Senjirin ta haifi 'yan uku - maza biyu da mace daya, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Edward Ajogun, ya ziyarci dangin a yankin Kemta na garin Abeokuta a ranar Laraba tare da mambobin kwamitin hulda da jama'a na 'yan sanda (PCRC).

Ajogun ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa yadda ya ba su kyautar jariran lafiya, yana mai bai wa dangin tabbacin ci gaba da ba su kulawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel