Kungiyar Afrika za ta karrama tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da Okonjo-Iweala a 2021

Kungiyar Afrika za ta karrama tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da Okonjo-Iweala a 2021

  • Africa Advancement Forum ta zabi mutanen da za ta karrama a shekarar bana
  • ‘Yan sahun gaba-gaba sun hada da Goodluck Jonathan da Ngozi Okonjo-Iweala
  • Za a ba wadannan manya lambar yabo ne a watan Agusta a birnin Accra, Ghana

Kungiyar nan ta Africa Advancement Forum za ta karrama tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, Premium Times ta fitar da wannan rahoto.

Dr. Goodluck Jonathan da takwaransa, tsohon shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, su na cikin wadanda kungiyar za ta karrama a shekara nan.

Kyautar kungiyar 'Africa Advancement Forum'

Wannan kungiya ta Africa Advancement Forum ta yi kaurin suna wajen samar da dangantaka tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa a fadin nahiyar Afrika.

KU KARANTA: Buhari ya karbi bakuncin Shugabar WTO, Dr. Okonjo-Iweala

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Kungiyar ta bada sanarwa cewa mutane su fito da sunayen wadanda su ke ganin sun cancanta a ba kyauta saboda cigaban da su ka kawo wa kasashen Afrika.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kan bada wannan kyauta da lambar yabon girmama wa wajen taron da kungiyar ta saba shirya wa a duk shekara, kamar yadda jaridar Head Topics ta bayyana.

Goodluck Jonathan, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala sun samu shiga

Dr. Goodluck Ebele Jonathan shi ne na farko a cikin wadanda mutane su ka zaba a shekarar bana.

Sauran wadanda su ka bi sahun tsohon shugaban Najeriyar wanda ya yi mulki tsakanin 2010 da 2015 sun hada da tsohuwar Ministarsa, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala.

Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Jonathan Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: WTO: Okonjo-Iweala ta maida martani bayan Amurka ta ki goyon bayanta

Baya ga Nana Akufo-Addo, akwai shugaban kamfanin Econet Group, Strive Masiyiwa, da tsohuwar shugabar kasar Liberiya, Ellen Johnson Sirleaf, a jerin.

Kara karanta wannan

Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Faɗi Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Ragowar sun hada da shugaban kamfanin jiragen sama na SRS Aviation, Sibongile Sambo da kuma shugaban kamfanin CEO ignite consulting, da dai sauransu.

Wani daga cikin jami’an kungiyar, Mudiaga Akakabota, ya bada wannan sanarwar. Akakabota ya ce za a yi wannan babban taro ne a ranar 20 ga watan Agusta, 2021.

Ngozi Okonjo-Iweala ta rike kujerar Ministar tattalin arziki a gwamnatin Goodluck Jonathan. A shekarar bana ta zama shugabar kungiyar kasuwanci ta Duniya.

A wancan lokaci, an yi ta kai ruwa-rana kafin Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar kungiyar kasuwancin na duniya saboda rashin goyon bayan kasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng