Yanzu-yanzu: Saura mataki guda, Ngozi Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar kungiyar kasuwancin duniya WTO

Yanzu-yanzu: Saura mataki guda, Ngozi Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar kungiyar kasuwancin duniya WTO

- Saura mataki daya kacal, Okonjo-Iweala ta samu goyon bayan yawancin kasashen duniya

- Sai dai Amurka ta lashi takobin cewa sam bata yarda ta zama ba

- Okonjo-Iweala yar Najeriya ce kuma 'yar Amurka

Tsohuwar ministar kudin Najeriya, Dr Ngozi Okonjo Iweala na gab da zama sabuwar Dirakta Janar na kungiyar kasuwancin duniya.

A cewar majiyoyi daga gamayyar kasashen Turai, za ta zama shugabar kungiyar ne bayan nasara kan Yoo Myung-hee, yar kasar Koriya ta kudu, idan akayi zaben ranar 9 ga Nuwamba.

DUBA NAN: Legas ba za ta iya daukan nauyin asarar da aka yi mata ba - Sanataocin jihohin Yarabawa

Yanzu-yanzu: Ngozi Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar kungiyar kasuwancin duniya WTO
Yanzu-yanzu: Ngozi Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar kungiyar kasuwancin duniya WTO Hoto:WTO
Asali: Facebook

KU KARANTA: An garkame Sojojin da aka kama suna zabgan matasan da suka saba dokar hana fita

Mun kawo muku rahoton cewa kasashe 27 da ke karkashin kungiyar Turai ta EU su na goyon bayan tsohuwar ministar tattalin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala a zaben WTO.

Jaridar Punch ta ce wadannan kasashe za su tsaya wa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala wajen ganin ta zama mace ta farko da ta rike shugabancin WTO.

Kasashen Turai da su ke tare da Okonjo-Iweala sun hada da Faransa, Jamus, Austriya, Beljika, Bulgariya, Kuroshiya, Czech, Italiya da kasar Denmark.

Sauran kasashen su ne: Saifiros, Estoniya, Finland, Girka, Hungariya, Ireland, Latviya, Lithuaniua, Luxembourg, Malta, Netherlands, da kuma Foland. Har ila yau har da kasashen Fotugal, Romaniya, Slovakiya, Sloveniya, Sifen, da Siwidin a jerin.

Rahotannin da mu ke samu shi ne kasashe 106 daga cikin 164 da ake da su a kungiyar WTO su na goyon bayan Dr. Okonjo-Iweala ta kawo kujerar.

Haka zalika kungiyar AU ta Afrika mai kasashe 55 ba ta tare da Yoo Myung-hee ta kasar Koriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel