Yanzu nan: Buhari ya karbi bakuncin sabuwar Shugabar WTO, Dr. Okonjo-Iweala

Yanzu nan: Buhari ya karbi bakuncin sabuwar Shugabar WTO, Dr. Okonjo-Iweala

- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi zama da Darektar kungiyar WTO

- Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta ziyarci Najeriya a karon farko bayan ta shiga ofis

- Ministoci sun yi wa Ngozi Okonjo-Iweala rakiya zuwa ofishin Shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Darekta-Janar ta kungiya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a fadar shugaban kasa, Aso Villa a birnin tarayya Abuja.

Fadar shugaban kasa ta fitar da wasu hotunan zaman Mai girma Muhammadu Buhari da tsohuwar Ministar tattalin arziki, Ngozi Okonjo-Iweala.

Wannan ne karo na farko da Ngozi Okonjo-Iweala ta ziyarci Najeriya tun da ta zama shugabar WTO, ita ce macen farko kuma bakar fata da ta hau kujerar.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta iso fadar Aso Villa ne da kimanin karfe 2:45 tare da wasu Ministoci.

KU KARANTA: Indiya za ta bi sahun Najeriya wajen harmata cinikin Bitcoin

Ministocin da su ka yi mata rakiya sun hada da: Ministan harkokin kasar waje, Geoffrey Onyeama, da takawaransa na kasuwanci, Otunba Niyi Adebayo.

Karamar Ministar kasuwanci ta Najeriya, Ambasada Maryam Katagum ta na cikin wannan tawaga.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ma’ikatan fadar shugaban kasar Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya tarbi Dr. Okonjo-Iweala da mutanen na ta.

Kafin yanzu tsohuwar Ministar ta ziyarci ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin Najeriya, inda Minista Zainab Ahmed ta yi mata kyakkyawar tarba.

KU KARANTA: ASUU ta gargadi Gwamnati a kan yajin-aiki saboda rashin albashi

Shugabar ta WTO ta iso Najeriya ne daga Geneva, kasar Switzerland a ranar Lahadi, ana sa ran za ta yi kwanaki a mahaifarta kafin ta koma bakin aikinta a ketare.

Dazu da safe mu ka ji labari cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gayyaci kungiyar IPMAN a zauna saboda ayi maganar tsaida sabon farashin fetur.

Shugaban kungiyar IPMAN, Mr. Chinedu Okoronkwo ne ya sanar da hakan a lokacin da ya yi hira da gidan talabijin na Arise News a karshen makon da ya gabata.

Bayan wannan taro, ana sa ran cewa jama’a za su san nawa litar fetur za ta koma a gidajen mai.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng