Cikakken bayani: Obasanjo ya magantu kan zargin kafa jam'iyya, ya ce ba ruwansa da siyasa

Cikakken bayani: Obasanjo ya magantu kan zargin kafa jam'iyya, ya ce ba ruwansa da siyasa

  • Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayyana gaskiyar zargin cewa zai kirkiri jam'iyyar siyasa
  • A baya an ruwaito cewa, wata majiya ta zargi tsohon shugaban kasar da kitsa kafa wata sabuwar jam'iyya
  • A bayansa, Obasanjo ya ce ba ruwansa da siyasa kuma bai da shirin kafa wata sabuwar jam'iyya

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce ya gama da siyasa kuma ba shi da niyyar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa kamar yadda majiyoyi suka gabatarwa manema labarai, Punch ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Litinin dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi, mai taken, ‘Obasanjo Bai Da Niyyar Kafa Jam'iyyar Siyasa’.

KARANTA WANNAN: Bayan shan ragargaza daga sojoji, Boko Haram da ISWAP sun sanyawa jama'a haraji

Da dumi-dumi: Obasanjo ya magantu kan zaben 2023, ya ce ba ruwansa da siyasa
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Akinyemi ya ce mai gidansa, wanda a halin yanzu yake a Kabul kasar Afghanistan, a matsayin bakon Shugaba Ashraf Ghani, ya bayyana cewa rahoton karya ne, yana mai cewa:

"Babu wani shiri na kafa sabuwar jam'iyyar siyasa a yanzu ko kuma nan gaba".

An ruwaito Obasanjo yana cewa,:

“A bangarena na duniya, idan ka ce sai da safe a wani wuri, ba za kuma ka koma can ba kace ina wuni. Wanda ya ba da rahoton hakan na bukatar ziyartar Yaba ta Hagu. Kuma wadanda suka yi imani da hakan za su iya gaskanta cewa uwayensu maza ne.
“Na gama damawa a siyasa, amma da irin matsayina a Najeriya da Afirka, ba tare da nuna girman kai ba a duniya ma, kofata a bude take ga kowane mutum ko kuma kungiya dake son neman ra’ayina ko shawara kan kowane batu ko matsala kuma zanyi kokari gwargwadon iko na, ba tare da kasancewa cikin tafiyar wannan mutum ko kungiyar ba.”

Wani bangaren sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga Daily Trust ta ce:

“Ya kamata wadanda suke son yin amfani da kofar baya su tilastawa Cif Obasanjo ya dawo a dama dashi cikin siyasa su mutunta zabinsa na zama mara kishin jam’iyya.
"A nasa bangaren, tsohon shugaban kasar zai ci gaba da taka rawar da yake takawa a matsayinsa na dattijon kasa da ya mayar da hankali kan bayar da shawarwari, goyon baya, ko mafita a duk inda ya dace a Najeriya, Afirka da ma duniya baki daya.

Olusegun Obasanjo ya kasance shugaban kasar Najeriya tun shekarar 1999 har zuwa shekarar 2007 a karkashin jam'iyyar PDP, wacce ta yi mulkin Najeriya na tsawon shekaru 16.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Buhari za ta samar wa ma'aikatan kashe gobara bindiga, ta fadi dalili

Obasanjo zai kirkiri sabuwar jam'iyya, ya zabi gwamnoni uku su jagoranceta

A wani labarin, Rahotanni da Legit.ng Hausa ke samu sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasar Najeriya, Obasanjo na aiki kan kirkirar wata sabuwar jam'iyyar da za ta dauki mambobin jam'iyyar adawa ta PDP da mai ci ta APC wadanda ke cikin damuwa gabanin zaben 2023 mai zuwa.

Wata majiya mai karfi ta fadawa jaridar Vanguard cewa Obasanjo ya gamsu cewa akwai yiwuwar manyan jam'iyyun siyasar biyu su shiga cikin rikice-rikice na doka da siyasa wanda zai bar su cikin mummunan hali, watakila ya kai su rasa jagorancin kasar a zaben na 2023.

Majiyar ta ce duk da cewa tsohon Shugaban kasar ya yayyaga katin zama dan jam’iyyar PDP tare da yin murabus daga siyasa, amma har yanzu yana himmatuwa wajen hada kan ’yan Najeriya don yin tasiri kan fitowar shugaban kasa na gaba, gwamnoni da sauran shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel