Rundunar 'Yan Sanda Ta Tabbatar 'Yan Bindiga Sun Sace Mutane 8 a Zaria
- Rundunar yan sanda ta jihar Kaduna ta tabbatar da sace mutane da yan bindiga suka yi a Saye, Zaria
- Kakakin yan sandan, ASP Muhammed Jalige ya ce misalin karfe 1.30 na dare ne yan bindigan suka kai harin
- Ya ce tawagar yan bindiga daya ta kai hari ofishin yan sanda yayin da ta biyun ta tafi asibitin na Saye domin sace mutanen
Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Kaduna, a ranar Lahadi ta tabbatar da sace mutane takwas daga rukunin gidajen ma'aikatan Cibiyar bincike kan cutar tarin TB da Kuturta da ke Zaria, jihar Kaduna, The Guardian ta ruwaito.
Vanguard ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar, ASP Muhammed Jalige ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi a Kaduna.
DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo
Sanarwar 'yan sanda game da sace mutum 8 a Saye, Zaria
Jalige ya ce, a farkon daren Asabar misalin karfe 1.30 na dare, wasu da ake zargin yan bindiga ne masu dimbin yawa suka kai hari hedkwatar ofishin yan sanda da ke Saye a Zaria.
Ya ce:
"A kokarinsu na cin galaba kan jami'an da ke aiki a ranar, sunyi karo da abin da ba su yi tsammani ba a yayin da suke yi musayar wuta tsakaninsu da yan sandan da ke aiki.
"Sai dai a lokacin da hakan na faruwa, wasu gungun yan bindigan suna can sun kai hari rukunin gidajen ma'aikatan Cibiyar bincike kan cutar tarin TB da Kuturta da ke Saye inda suka yi awon gaba da mutum takwas zuwa wani wurin da ba a sani ba a yanzu."
Ya cigaba da cewa an samu kwankon harsahin bindiga 23 da harsashin GPMG tare da wasu kwankon harsahin mai tsawon 7.62x39m a wurin da abin ya faru.
Jalinge ya kara da cewa a halin yanzu rundunar ta baza jami'anta domin ceto wadanda aka sace da kama masu laifin.
Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba da Ɗalibai da dama a Kaduna
A wani labarin, Yan bindiga a ranar Litinin, sun yi awon gaba da ɗalibai da dama a makarantar Bethel Baptist dake Maraban Rido, ƙaramar hukumar Chukun, jihar Kaduna.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Leadership.
Yace yan bindigan sun mamaye makarantar da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda suka fara harbi a sama kafin daga bisani su sace ɗaliban, kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.
Asali: Legit.ng