Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Ruwan Wuta Kan Wasu Yan Bindiga da Suka Kai Hari Caji Ofis

Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Ruwan Wuta Kan Wasu Yan Bindiga da Suka Kai Hari Caji Ofis

  • Wasu yan bindiga sun kai hari caji ofis ɗin yan sanda a ƙaramar hukumar Udung Uko ranar Asabar da daddare
  • Yan sandan dake aiki a wannan lokacin sun yi namijin ƙoƙarin wajen maida martani kan maharan
  • Kakakin yan sandan jihar, Macdon, ya tabbatar da lamarin, yace babu wanda ya rasa ransa

Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kai hari caji ofis ɗin yan sanda dake ƙaramar hukumar Udung Uko, jihar Akwa Ibom, ranar Asabar da daddare, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Hoton Gwamna Zulum Yana Huɗa a Gonarsa, Ya Kai Ziyara Sansanin Yan Gudun Hijira

Rahoto ya nuna cewa maharan sun kai hari caji ofis ɗin a kan motoci, inda suka buɗe wuta kan jami'an tsaron dake wurin.

Wata majiya da ya nemi a sakaya sunansa ya faɗawa manema labarai a Uyo, cewa yan sanda uku sun samu raunuka yayin da suka yi ƙoƙarin maida martani.

Yan bindiga dun kai hari caji ofis
Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Ruwan Wuta Kan Wasu Yan Bindiga da Suka Kai Hari Caji Ofis Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace: "Wasu yan bindiga sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi a hedkwatar yan sanda dake ƙaramar hukumar Udung Uko da daddare."

"Gwarazan jami'an dake bakin aiki sun maida martani kan maharan, a yayin fafatawar ne jami'ai uku suka samu raunukan harbi."

Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin

Kakakin yan sanda na jihar Akwa Ibom, Odiko Macdon, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace babu wanda ya rasa rayuwarsa.

Macdon ya ƙara da cewa yan bindigan sun kai hari ofishin ne a cikin mota ƙirar Sienna Toyota, inda suka buɗe wuta.

KARANTA ANAN: Ba Zan Taɓa Mantawa da Fasto Tunde Bakare ba, El-Rufa'i Ya Faɗi Alƙarsa da Faston Coci

Ya kuma yaba wa jami'an yan sandan dake aiki a wannan lokacin bisa namijin ƙoƙarin da suka yi na maida martani kan maharan.

"An yi ƙoƙarin kai hari ɗaya daga cikin ofishin mu a ƙaramar hukumar Udung Uko, amma jami'an yan sanda sun maida martani, babu wanda ya rasa ransa," inji shi.

A wani labarin kuma Bayan Komawarsa APC, Gwamna Matawalle Ya Sallami Dukkan Mashawartansa Na Musamman

Gwamna Matawalle na jihar Zamfara, ya sallami gaba ɗaya masu ba shi shawara na musamman banda mutum ɗaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bayan ya sauya sheƙa zuwa APC a hukumance ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel