Bayan Ganawa da Nnamdi Kanu, Lauya Ya Faɗi Halin da Ya Shiga Kafin a Dawo da Shi Najeriya

Bayan Ganawa da Nnamdi Kanu, Lauya Ya Faɗi Halin da Ya Shiga Kafin a Dawo da Shi Najeriya

  • Ifeanyi Ejiofor, lauyan dake kare shugaban haramtacciyar ƙungiyar taware IPOB, Kanu, ya samu ganawa da shi
  • Lauyan ya bayyana cewa an damƙe wanda yake karewa tun 18 ga watan Yuni, inda aka tsare shi tare da azabtarwa
  • Har yanzun gwamnatin tarayya bata ce komai ba game da kasar da ta kamo Nnamdi Kanu

Lauyan dake kare, Nnamdi Kanu, shugaban ƙungiyar taware IPOB, Ifeanyi Ejiofor, yace bayan an cafke Nnamdi sai da aka tsare shi na tsawon kwanaki 8 a Kenya, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yadda Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i Ya Cire Ɗansa Daga Makarantar Gwamnati a Sirrince

Ejiofor ya bayyana haka ne bayan ya kaiwa Kanu ziyara a ofishin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Lauya ya gana da Nnamdi Kanu
Bayan Ganawa da Nnamdi Kanu, Lauya Ya Faɗi Halin da Ya Shiga Kafin a Dawo da Shi Najeriya Hoto: dw.com
Asali: UGC

Yace: "Wasu jami'an yan sanda na musamman a ƙasar Kenya sun ɗauke wanda nake kare wa, Mazi Nnamdi Kanu, a ranar 18 ga watan Yuni, 2021, a filin tashi da saukar jiragen sama, inda suka tasa ƙeyarsa zuwa wani wuri da ba'a bayyana ba."

"An azabtar da shi wanda hakan ya taɓa lafiyar jikinsa, sannan an tsare shi ba bisa ƙa'ida ba na tsawon kwanaki 8 kafin daga bisa ni a dawo da shi Najeriya."

"Mun gano cewa suna bincikarsa ne a kan wani laifi yayin da yake a tsare a hannunsu, amma daga baya sai suka gano ba shi da laifi, sannan suka miƙa shi a hannun takwarorinsu na Najeriya."

"Gwamnatin Kenya na da hannu a ɗauke Kanu, tsare shi ba bisa ƙa'ida ba da azabtar da shi kafin a miƙa shi ga jami'an tsaron Najeriya." inji shi.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Gwamna Zulum Ya Shilla Ƙasar Nijar, Ya Sa Labule da Shugaba Bazoum

Gwamnatin Kenya tace ba'a ƙasar ta aka kama shi ba

Duk da cewa gwamnatin tarayya taƙi sanar da inda ta damƙo Nnamdi Kanu, amma ɗan uwansa, Kingsley Kanu, yace a Kenya a kamo shi.

Hakanan Kuma, darakta janar na hukumar kula da shige da fice na ƙasa Kenya, Alexander Muteshi, yace sam ba su san da labarin kama Kanu a ƙasar su ba.

A wani labarin kuma Ba Zamu Huta ba Har Sai Mun Tabbatar da Yan Najeriya Na Bacci da Ido Biyu, IGP

IGP Usman Baba, ya bayyana wa yan majalisar wakilai cewa hukumarsa na aiki ba dare ba rana domin bada tsaro ga yan Najeriya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Baba ya faɗi haka ne yayin da ya bayyana gaban kwamitin kula da ayyukan hukumar yan sanda ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel