Yadda Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i Ya Cire Ɗansa Daga Makarantar Gwamnati a Sirrince

Yadda Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i Ya Cire Ɗansa Daga Makarantar Gwamnati a Sirrince

  • Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya cire dansa daga makarantar gwamnati bayan ya sanya shi
  • Ana ganin dai gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne saboda yawaitar sace ɗalibai a makarantun jihar
  • Mazauna Kaduna sun bayyana rashin jin daɗinsu kan cire, Al-sadiq, daga makarantar gwamnati

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya cire ɗansa daga makarantar gwamnati a sirrin ce, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Yayin da gwamnan ya sanya ɗansa, Al-Sadiq, a makarantar gwamnati a bayyane, mutane da dama sun yi tsokaci a kan matakin gwamnan, amma cire shi da ka yi a sirrin ce yasa wasu ke ganin wannan yaudara ce da kuma rashin ingancin makarantun.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Gwamna Zulum Ya Shilla Ƙasar Nijar, Ya Sa Labule da Shugaba Bazoum

Babu wani ƙwakkwaran dalili da yasa gwamnan ya cire ɗansa, amma wasu masu tsokaci sun bayyana cewa saboda yawaitar satar mutane a makarantu ne yasa gwamnan ɗaukar wannan matakin.

Gwamna El-Rufa'i ya cire ɗansa daga makarantar gwamnati
Yadda Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i Ya Cire Ɗansa Daga Makarantar Gwamnati a Sirrince Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Wasu kuma na ganin iyalansa ne suka matsa sai ya cire ɗan nashi ko kuma makarantun gwamnatin ne ba su da inganci.

Mazauna yankin da makarantar take, sun nuna rashin jin daɗinsu bisa matakin gwamnan na zare ɗansa bayan ya fara karatunsa tare da yaran talakawa.

A baya mutane da dama na ganin sanya ɗan El-Rufa'i a makarantar gwamnati wata dama ce da zaisa a gyara makarantun.

Mutanen Kaduna sun nuna rashin jin daɗinsu

Mazauna jihar Kaduna musamman waɗanda ke zaune a yankin makarantar da aka sanya El-Sadiq, sun bayyana damuwarsu kan matakin cire yaron.

Wani mai suna, Ibrahim Yero, yace:

"Bamu ji daɗin cire shi ba, saboda hakan ya nuna cewa saka yaron da aka yi a baya duk yaudara ce kawai."

"Ya kamata shugabanni sun rinƙa cika maganganunsu da alƙawurran su, bayan gwamna ya cire ɗansa daga makaranyar, yanzun kuma ya koma yana ƙara yawan kuɗin makaranta da korar malamai."

"Na kasa fahimtar inda gwamnan ya sa gaba, wani ya taimaka ya masa magana hakanan dan Allah."

Har yanzun gwamnatin jihar Kaduna ba ta yi martani kan lamarin cire ɗan gwamna El-Rufa'i ba.

KARANTA ANAN: Wasu Fusatattun Mata da Ƙananan Yara Sun Toshe Hanyar Sokoto-Gusau

Ranar da aka sanya yaron a makaranta

Lokacin da gwamna El-Rufa'i tare da matarsa, Ummi, suka saka ɗan su mai shekara 6 a makarantar gwamnati a 2019, yan Najeriya da dama sun yaba wa gwamnan.

Mutane da dama sun jinjinawa gwamnan tare da fatan cewa Malam El-Rufa'i ya ɗakko hanyar gyara ilimi a jihar Kaduna.

A wancan lokaci, wannan matakin gwamnan ya ƙara wa iyaye da dama ƙwarin guiwa cewa makarantun gwamnati suna da kyau, kuma yayansu zasu iya samun ilimi mai inganci.

A wani labarin kuma Yan Majalisa Sun Yi Fatali da Buƙatar Ɗage Dokar Hana Twitter

Majalisar wakilan tarayya ta yi watsi da buƙatar ɗage dokar gwamnatin tarayya ta hana amfani da twitter, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne yayin da take nazari kan rahoton kwamitocinta da suka gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel