Da Ɗuminsa: Yan Majalisa Sun Yi Fatali da Buƙatar Ɗage Dokar Hana Twitter

Da Ɗuminsa: Yan Majalisa Sun Yi Fatali da Buƙatar Ɗage Dokar Hana Twitter

  • Majalisar wakilan tarayya ta yi watsi da buƙatar ɗage dokar gwamnatin tarayya ta hana amfani da twitter
  • Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne yayin da take nazari kan rahoton kwamitocinta da suka gudanar da bincike
  • A watan da ya gabata ne gwamnatin tarayya da sanar da hana amfani da dandalin sada zumunta na twitter

Yan majalisar wakilan tarayya sun yi watsi da buƙatar ɗage dokar hana amfani da twitter a Najeriya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yan majalisar sun yi watsi da kudurin ne yayin da suke sauraron rahoton kwamitin da aka ɗorawa alhakin bincike kan lamarin.

KARANTA ANAN: Matawalle Ya Yi Magana Kan Kisan Ɗan Majalisar Jiharsa, Ya Bayyana Alhaninsa

A yayin da suke nazari kan rahoton, mataimakin shugaban marasa rinjayi a majalisar, Toby Okechukwu, ya bada shawarar a yi gyara a ɗaya daga cikin shawarwarin da aka gabatar.

Yan majalisa sun yi fatali da kudirin dawo da twitter
Da Ɗuminsa: Yan Majalisa Sun Yi Fatali da Buƙatar Ɗage Dokar Hana Twitter Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hon. Okechukwu, yace: "Ya kamata gwamnatin tarayya ta duba illar da hana amfani da twitter yayi wa yan Najeriya waɗanda suka dogara da shafin domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, ta janye dokar hana amfani da twitter."

Wani ɗan majalisa ɗaya ya goyi bayanshi, amma duk da haka mafi yawncin yan majalisun sun yi fatali da ƙudirin na su bayan an kaɗa kuri'a.

Majalisa ta umarci kwamitinta su gudanar da bincike

Idam zaku iya tunawa, a kwanakin baya majalisar ta umarci kwamitin yaɗa labarai, ICT, fasahar zamani, da kwamitin shari'a su binciki dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin dakatar da twitter.

KARANTA ANAN: Ba Zamu Huta ba Har Sai Mun Tabbatar da Yan Najeriya Na Bacci da Ido Biyu, IGP

A watan da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta bayyana dakatar da amfani da shafin twitter a Najeriya busa zarginsa da aikata ba dai-dai ba.

A wani labarin kuma Mun San Inda Yan Bindiga Suka Ɓoye Ɗaliban Islamiyyar Tegina, Gwamnatin Neja

Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa ta san wurin da yan bindiga suka ɓoye ɗaliban da suka sace a Tegina, kamar yadda the nation ta ruwaito.

A cewar gwamnatin, a halin yanzu ta na tattaunawa ne da ɓarayin, amma ba zata biya kuɗin fansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel