Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke mutum 7, sun sace wasu 10 a sabon hari

Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke mutum 7, sun sace wasu 10 a sabon hari

  • Rayuka bakwai aka rasa yayin da aka sace wasu mutum 10 a sabon harin 'yan bindiga a jihar Kaduna
  • Miyagun 'yan bindigan sun kai harin ba-zata kananan hukumomin Chikun, Kajuru da Giwa dake jihar Kaduna
  • Sun tabbatarwa da mazauna yankunan cewa manyansu zasu dawo, lamarin da ya firgita mazauna yankunan

A kalla mutum bakwai aka kashe yayin da aka sace wasu goma a mabanbantan hare-hare da 'yan bindiga suka kai kananan hukumomin Chikun , Kajuru da Giwa a jihar Kaduna.

Daga cikin jama'ar akwai wasu hudu da aka sace tare da harbewa a yankin Tsohon Gayan dake karamar hukumar Chikun ta jihar yayin da wasu biyu aka kashesu a tashar Iri dake karamar hukumar Kajuru.

KU KARANTA: Bidiyon Hanan Buhari cikin taron Turawa ta garzaya karbar kwalin digirinta na 2

Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke mutum 7, sun sace wasu 10 a sabon hari
Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke mutum 7, sun sace wasu 10 a sabon hari. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Rashida mai sa'a ta yi bayani dalla-dalla kan rade-radin aurenta da Iyan Tama

Moses Matthew, wani mazaunin tashar Iri dake karamar hukumar Kajuru ta jihar, ya sanar da ChannelsTv cewa 'yan bindiga sun dira yankin wurin karfe 1 na dare dauke da miyagun makamai kuma sun fara harbe-harbe.

Ya ce mazauna yankin sun ji karar harbe-harben, lamarin da yasa suka dinga ihu yayin da 'yan bindiga suka yi nasarar sace mutum 10.

"Suna zuwa suka shiga gidan jama'a, daga karshe sai muka gane sun sace mutum 10 tare da kashe wasu 2," yace.

“Duk da haka, jama'ar nan na cewa karamar kungiya ce, manyansu na nan zuwa. Amma kuma bamu san me muka yi musu ba."

Firgitattun mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta tsananta tsaro tare da tura jami'an tsaro yankin, Channels TV ta ruwaito.

A bangarensa, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya jagoranci jami'an tsaro zuwa yankin a ranar Lahadi inda ya kwatanta harin da na rashin imani.

Ya jaddada cewa gwamnatiin jihar tare da hadin guiwar jami'an tsaro za ta yi duk abinda za ta iya wurin damko wadanda suka yi barnar tare da tsayar da cigaban harin.

A wani labari na daban, jami'an tsaro na farin kaya sun yi ikirarin cewa wasu maza da suke tsammanin masu tsaron Sunday Igboho ne sun yi musayar wuta da jami'ai a yayin samamen da suka kai gidan mai assasa samar da kasar Yarabawa a Ibadan da safiyar Alhamis.

Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis bayan kama mutum 13 a gidan Igboho, Channels TV ta ruwaito.

Kamar yadda Afunanya ya sanar, samamen ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu na cewa ana tara makamai a gidan Igboho, lamarin da yasa ake samun rashin zaman lafiya a yankin kudu maso yamma.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel