Bidiyon Hanan Buhari cikin taron Turawa ta garzaya karbar kwalin digirinta na 2

Bidiyon Hanan Buhari cikin taron Turawa ta garzaya karbar kwalin digirinta na 2

  • Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan Buhari, tana daya daga cikin mutum 1200 da suka kammala digirinsu na biyu daga Royal College a Ingila
  • Hanan Buhari ta auri Muhammad Turad Sha'aban a shekarar da ta gabata bayan ta kammala digirinta na farko a fannin hoto
  • A wani bidiyo mai bada sha'awa, Hanan ta samu tafi da sowa daga jama'a yayin da ta tashi ta garzaya karbar kwalin digirinta na biyu

Diyar shugaban kasan Najeriya, Hanan Buhari, a ranar Talata, 29 ga watan Yuni ta karba kwalinta na digiri na biyu da ta kammala a London.

Hanan wacce ta kammala digirinta na farko da takarda mai daraja ta daya daga Royal College of Arts dake London a 2019, ta kammala digirinta na biyu a wannan shekarar.

KU KARANTA: Gangamin Yarabawa a Legas: Igboho yace bashi da karfin yakar gwamnatin tarayya

Bidiyon Hanan Buhari cikin taron jama'a ta garzaya karbar kwalin digirinta na 2
Bidiyon Hanan Buhari cikin taron jama'a ta garzaya karbar kwalin digirinta na 2. Hoto daga @lindaikejiblog @Bellanaija
Asali: Instagram

KU KARANTA: Dalla-dalla: Da na "hannun daman" Nnamdi Kanu aka hada kai aka kama shi

A wani bidiyo da mahaifiyar Hanan, Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga matashiyar ta tashi tsaye yayin da ake tafi da jinjina mata yayin da za ta karba takardarta.

Hanan wacce take daya daga cikin dalibai 1200 da aka yaye a makaranta, ta dagawa wasu hannu yayin da ake mata tafi ita kuwa tana tafe cike da birgewa.

'Yan Najeriya sun yi martani

Bidiyon ya janyo cece-kuce daban-daban a kafafen sada zumunta.

@okonobohwilfred tsokaci yayi da: "A nan suke salwantar da kudadenmu... shugabannin kawai, jami'o'inmu sun yi muni."

@uc_amaka ta ce: "Ai da taje jami'ar gwamnatin tarayya ko ta jiha domin ta nuna mahaifinta yana aiki."

@ollahbabe cewa tayi: "Shugabannin kasa nawa ne 'ya'yansu ke karatu a kasar nan? Gwamnati bata damu da tsarin makarantunmu ba. Saboda a karshe 'ya'yansu kasashen ketare suke tafiya."

A wani labari na daban, a ranar Laraba da ta gabata, jam'iyyar APC tayi martani kan zargin da ake yi na cewa komen da wasu gwamnonin PDP ke yi zuwa APC hanya ce ta buga magudin zabe a 2023.

Premium Times ta ruwaito cewa a wata takarda da APC ta fitar ta hannun sakataren jam'iyyar na kasa, John Akpanudoedehe, ta ce 'yan jam'iyyar PDP na barin jam'iyyar ne tare da komawa APC saboda rashin adalci da suke fuskanta da kuma rashin damokaradiyyar cikin gida.

Wannan martanin ya biyo bayan zargin da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus yayi bayan sauya shekar da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel