Luguden wuta yaran Igboho suka fara mana da muka je bincike, DSS

Luguden wuta yaran Igboho suka fara mana da muka je bincike, DSS

  • Jami'an hukumar DSS sun ce luguden wuta mukarraban Sunday Igboho suka fara musu
  • Sun ce shida daga cikin mutum tara da suka tarar suna dauke da bindiga kirar AK47
  • Kamar yadda Afunanya yace, tsagerun sun harbi jami'i daya a hannun hagu yayin arangamar

Jami'an tsaro na farin kaya sun yi ikirarin cewa wasu maza da suke tsammanin masu tsaron Sunday Igboho ne sun yi musayar wuta da jami'ai a yayin samamen da suka kai gidan mai assasa samar da kasar Yarabawa a Ibadan da safiyar Alhamis.

Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis bayan kama mutum 13 a gidan Igboho, Channels TV ta ruwaito.

Kamar yadda Afunanya ya sanar, samamen ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu na cewa ana tara makamai a gidan Igboho, lamarin da yasa ake samun rashin zaman lafiya a yankin kudu maso yamma.

KU KARANTA: Sauya Sheka: Rashin damokaradiyyar cikin gida ta sa gwamnoni ke tserewa, APC ga PDP

Luguden wuta yaran Igboho suka fara mana da muka je bincike, DSS
Luguden wuta yaran Igboho suka fara mana da muka je bincike, DSS. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Mutum 9 'yan gida daya sun sheka lahira bayan cin abinci mai guba a Zamfara

"A yayin da muka kusanci gidansa, wasu mutum tara da ake zargin mukarraban Igboho ne sun dinga mana luguden wuta. Shida suna dauke da AK47 sauran ukun kuma da wata bindiga," Mai magana da yawun DSS yace.

"A yayin musayar wutan, mun sheke biyu yayin da muka damke sauran. Jami'inmu daya ne wani daga ciki ya harba a hannun dama. Amma yanzu ya samu taimakon likitoci kuma yana samun sauki.

"Musayar wutan da muka yi ya dauka sa'a daya, lamarin da yasa Igboho ya samu damar tserewa. A halin yanzu ana nemansa ido ruwa jallo."

An kama mutum 13 daga cikin tsagerun Igboho, 12 maza da mace daya. An samu miyagun makamai a cikin gidansa, Channels TV ta tabbatar.

A wani labari na daban, wata kungiya mai suna International Society for Civil Liberties and Rule of Law, ta ce "makusanta kuma shakikan Nnamdi Kanu ne suka saka masa tarko a kan wata matsala dake tsakaninsu."

Kungiyar ta ce kamen da aka yi wa Kanu a filin jirgin sama da farko an yi zaton karamin lamari ne tsakaninsa da jami'an hukumar shige da fice, wanda daga bisani ya bayyana cewa da gangan ne kuma daga bisani aka saka jami'an diflomasiyya na Najeriya.

A yayin bada bayani game da yadda aka kama Kanu, takardar da shugabannin kungiyar Emeka Umeagbalasi, Obianuju Igboeli, da Chidimma Udegbunam, ta ce, "an janyo hankalon jami'an diflomasiyya na Najeriya da kuma jami'an tsaro a Nairobi, babban birnin kasar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: