Rashida mai sa'a ta yi bayani dalla-dalla kan rade-radin aurenta da Iyan Tama
- Jaruma Rashida Adamu Abdullahi ta musanta rade-radin dake yawo na cewa za ta angwance da Iyan-Tama
- Kamar yadda ta sanar, ta ce fastar wani fim suka yi hotunan shine ta wallafa a shafinta na Instagram
- A cewarta, ta dauka furodusa Hamisu Lamido Iyan-Tama tamkar uba kuma akwai mutuntawa tsakaninsu
Sananniyar jarumar Kanyywoood, Rashida Adamu Abdullahi wacce ake kira da Mai Sa'a ta yi fatali da cece-kucen dake yawo ne cewa zata angwance tare da furodusa Hamisu Lamido Iyan-Tama.
Jama'a da yawa sun ta zaton aure manyan furodusoshin biyu za su yi bayan wasu hotunansu sun bayyana kuma jarumar ta wallafa a Instagram.
Sai dai jaruma Rashida ta zanta da Mujallar Fim inda ta tabbatar da cewa babu wani batun soyayya dake tsakaninta da babban furodusan, lamarin duk shiri ne.
KU KARANTA: Dalla-dalla: Da na "hannun daman" Nnamdi Kanu aka hada kai aka kama shi
KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƙanin Nnamdi Kanu ya bayyana kasar da aka kama yayan shi a Afrika
Rashida ta ce tsakaninta da furodusa Iyan-Tama girmamawa ce kuma ta dauke shi tamkar mahaifinta.
A cewarta, "Kowa ya san Iyan-Tama darakta ne, furodusa kuma jarumi ne a masana'antar. A gefe daya kuma uba ne. Tsakanina da Iyan-Tama kawai girmamawa da mutuntawa kwarai da gaske domin a yayin da yayi fina-finansa ban shigo industiri ba.
"Jama'a suna ta cewa zan auri Iyan-Tama amma ba haka bane. Fim din shi ne za a fitar wanda ya sha alwashin dawo da ni masana'antar a matsayin jaruma. Da farko na ce ba zan yi ba amma daga bisani na amince. Saboda haka muka yi wasu hotuna kuma za a saka a fastar fim din.
“Sunan fim din saura kiris kuma ko da na wallafa hotunan a shafina na Instagram na rubuta Saura Kiris."
A wani labari na daban, kafin zuwan ranar gangamin da Yarabawa zasu yi a jihar Legas na ranar 3 ga watan Yuli, mai rajin kare hakkin Yarabawa, Sunday Adeyemo ya tabbatar da cewa zasu yi gangamin cikin lumana da kwanciyar hankali saboda bashi da karfin yakar gwamnatin tarayya da shugabannin siyasa.
Adeyemo wanda ake kira da Igboho ya sanar a sabon bidiyon da ya fitar cewa za a yi gangamin duk rintsi ko tsanani, Vanguard ta ruwaito.
Vanguard ta wallafa cewa, yayi dogaro da irin gangamin da suka yi a jihohin Ogun, Oyo, Ondo da Osun inda yace gangamin Legas zai kasance na lumana kamar yadda aka yi a sauran jihohin kudu maso yamma.
Asali: Legit.ng