Boko Haram: Sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda sanye da kayan sojoji a Borno

Boko Haram: Sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda sanye da kayan sojoji a Borno

  • 'Yan ta'addan ISWAP masu tarin yawa sanye da kayan sojoji sun sheka lahira bayan arangamar su da jami'an tsaro
  • 'Yan ta'addan sun tare wasu 'yan sanda a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Juma'a
  • Tuni dakarun sojin sama suka bayyana da jiragen yaki inda suka yi wa 'yan ta'addan luguden wuta tare da sheke wasu

Mayakan ISWAP wadanda ba a san yawansu ba sun sheka lahira bayan arangamar da suka yi da jami'an tsaron hadin guiwa a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno.

'Yan ta'addan wadanda aka gani cikin kayan sojoji sun kai farmaki tare da budewa wata tawagar jami'an 'yan sanda wuta a yammacin Juma'a yayin da suke dawowa daga Buni Yadi kusa da Auno-Garin Kuturu a karamar hukumar Kaga.

An gano cewa 'yan ta'addan sun kwace wata mota daya da take mallakin jami'an tsaron, TheCable ta ruwaito.

KU KARANTA: Bidiyon Hanan Buhari cikin taron Turawa ta garzaya karbar kwalin digirinta na 2

Boko Haram: Sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda sanye da kayan sojoji a Borno
Boko Haram: Sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda sanye da kayan sojoji a Borno. Hoto daga thecableng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Rade-radin rushewa: Ma'aikata sun yi gudun ceton rai a hedkwatar APC ta Abuja

Amma kuma martanin gaggawa da dakarun sojin sama na runduna ta 212, bataliya ta 73 tare da runduna ta 134 da bataliya ta 199 suka kai ya janyo ajalin 'yan ta'addan.

Wata majiya a rundunar sojin kasan ta ce sojojin sun bayyana ta jiragen yaki inda suka dinga ragargazar 'yan ta'addan a kauyen malam Fantari.

Wannan ragargazar ta janyo ajalin 'yan ta'adda masu tarin yawa a motocin yaki biyu, TheCable ta ruwaito.

Sauran da suka samu miyagun raunika sun bar ababen hawansu inda suka nemi hanyar tsira.

"Sai dai cike da rashin jin dadin lamarin, dan sanda daya ya mutu a take kuma an samu wasu gawawwaki biyu yayin da jami'an tsaro suka je duba yankin," majiyar tace.

"Abun hawan da aka samu yana hannun rundunar 'yan sandan jihar Borno."

A wani labari na daban, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kama Fulani makiyaya masu yawo da bindiga ballantana shugabannin Miyetti Allah kamar yadda ya kama shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Ortom wanda ya bayyana cewa a kasar ketare aka cafko Kanu, ya zargi cewa Miyetti Allah ce ke aiwatar da miyagun hare-hare a jihar Benue.

A yayin jaddada cewa bashi da wata matsala da kamen shugaban IPOB, ya kara da cewa yaki da ta'addanci da dukkan laifuka ya dace a yi shi ne ba tare da bangaranci ba.

A wani labari na daban, jami'an tsaro na farin kaya sun yi ikirarin cewa wasu maza da suke tsammanin masu tsaron Sunday Igboho ne sun yi musayar wuta da jami'ai a yayin samamen da suka kai gidan mai assasa samar da kasar Yarabawa a Ibadan da safiyar Alhamis.

Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis bayan kama mutum 13 a gidan Igboho, Channels TV ta ruwaito.

Kamar yadda Afunanya ya sanar, samamen ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu na cewa ana tara makamai a gidan Igboho, lamarin da yasa ake samun rashin zaman lafiya a yankin kudu maso yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: