Rade-radin rushewa: Ma'aikata sun yi gudun ceton rai a hedkwatar APC ta Abuja
- Hankulan ma'aikata, jami'an tsaro da na manema labarai a sakateriyar APC dake Abuja ya tashi
- Hakan ya faru ne bayan an fara rade-radin cewa ginin zai rushe sakamakon girgiza da ya fara
- Sai dai wani ganau ya ce duk shirme ne, babu wata alamar girgiza da suka ji, zance ne kawai
An shiga tashin hankali a sakateriyar jam'iyyar APC a ranar Alhamis a garin Abuja bayan an dinga rade-radin cewa ginin zai rushe.
Sakateriyar APC ta kasa tana nan a lamba 40, titin Blantyre dake Wuse 11, Abuja, babban birnin tarayya, Daily Trust ta ruwaito.
Wani ganau ba jiyau ba wanda ya zanta da manema labarai, ya ce daya daga cikin ma'aikatan dake bene hawa na hudu ya koka da yadda ginin ke rawa.
KU KARANTA: Dalla-dalla: Da na "hannun daman" Nnamdi Kanu aka hada kai aka kama shi
KU KARANTA: Sauya Sheka: Rashin damokaradiyyar cikin gida ta sa gwamnoni ke tserewa, APC ga PDP
Ya ce wannan lamarin ne ya ja hankalin mutane inda dukkan jami'an jam'iyyar suka fara gudun ceton rai.
Ma'aikatan sakateriya, 'yan jarida, jami'an tsaro da sauran ma'aikata sun dinga gudun ceton rai.
Wani ganau ya ce, "Abin takaici ne yadda lamarin ya kai har kafafen sada zumunta. Babu wani abu kamar rushewar gini. Babu wani abu makamancin girgiza da ginin yake.
"Mun dade a nan wurin don mun yi shekaru masu yawa amma babu abu makamancin haka da ya faru. Ina dai tunanin wani abu ne na daban," yace.
Daily Trust ta ruwaito cewa dukkan ma'aikatan da suka sauko daga ginin mai hawa hudu basu koma ba.
A wani labari na daban, tashin hankali ya fada kauyen Jangeme dake karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara lokacin da wasu 'yan gida daya suka sheka lahira bayan cin guba da suka yi a abinci.
Wani kawun mamatan mai suna Abdullahi Bello ya sanar da Daily Trust cewa yaran sun mutu ne bayan 'yar uwarsu da ta kawo musu ziyara daga gidan mijinta ta yi musu Tuwon dawa.
Bello ya ce: "Yayin da ta zo gida, ta debo dawa daga rumbu kuma ta kai nika. Wani beran masar da ake kiwo a gidan ya mutu bayan ya ci garin tun kafin ta fara yin tuwon."
Asali: Legit.ng