Kamar yadda ka kama Kanu, ka kama shugabannin Miyetti Allah, Ortom ga Buhari

Kamar yadda ka kama Kanu, ka kama shugabannin Miyetti Allah, Ortom ga Buhari

  • Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya yi kira ga Buhari da ya kama shugabannin Miyetti Allah kamar yadda yayi wa Nnamdi Kanu
  • Gwamnan yace bashi da matsala da kamen Kanu amma kamata yayi a yaki dukkan laifuka da ta'addanci a kasar nan
  • Ortom yace akwai matukar takaici yadda makiyaya ke cin karensu babu babbaka amma babu wanda ke dubansu

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kama Fulani makiyaya masu yawo da bindiga ballantana shugabannin Miyetti Allah kamar yadda ya kama shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Ortom wanda ya bayyana cewa a kasar ketare aka cafko Kanu, ya zargi cewa Miyetti Allah ce ke aiwatar da miyagun hare-hare a jihar Benue.

KU KARANTA: Rashida mai sa'a ta yi bayani dalla-dalla kan rade-radin aurenta da Iyan Tama

Kamar yadda ka kama Kanu, ka kama shugabannin Miyetti Allah, Ortom ga Buhari
Kamar yadda ka kama Kanu, ka kama shugabannin Miyetti Allah, Ortom ga Buhari. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Sauya Sheka: Rashin damokaradiyyar cikin gida ta sa gwamnoni ke tserewa, APC ga PDP

A yayin jaddada cewa bashi da wata matsala da kamen shugaban IPOB, ya kara da cewa yaki da ta'addanci da dukkan laifuka ya dace a yi shi ne ba tare da bangaranci ba.

Ya ce bai dace a hukunta wasu ba tunda makiyaya dake kashe jama'a suna cigaba da cin karensu babu babbaka.

Kamar yadda yace, abun takaici ne yadda Miyetti Allah ke kiran Nnamdi Kanu da dan ta'adda, duk da yana yaki ne domin samun 'yancin yankinsu.

Gwamnan ya jaddada cewa Miyetti Allah gagarumar kungiyar ta'addanci ce.

Gwamna Ortom ya kara da bayyana cewa miyagun makiyaya sun haifar da tsananin matsantawa da takura ga jihar Benue da jama'arta.

A wani labari na daban, tashin hankali ya fada kauyen Jangeme dake karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara lokacin da wasu 'yan gida daya suka sheka lahira bayan cin guba da suka yi a abinci.

Wani kawun mamatan mai suna Abdullahi Bello ya sanar da Daily Trust cewa yaran sun mutu ne bayan 'yar uwarsu da ta kawo musu ziyara daga gidan mijinta ta yi musu Tuwon dawa.

Bello ya ce: "Yayin da ta zo gida, ta debo dawa daga rumbu kuma ta kai nika. Wani beran masar da ake kiwo a gidan ya mutu bayan ya ci garin tun kafin ta fara yin tuwon."

Asali: Legit.ng

Online view pixel