Sunday Igboho: Gwamnonin kudu maso yamma sun gudanar da taron gaggawa

Sunday Igboho: Gwamnonin kudu maso yamma sun gudanar da taron gaggawa

  • An rahoto cewa gwamnoni daga yankin kudu maso yammacin Najeriya sun gana kan matakin rashin tsaro a Najeriya
  • An ce sun tattauna ne game da lamarin dan gwagwarmayan Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda ake kira Sunday Igboho
  • Jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun mamaye gidan Igboho a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli

Wani rahoto da jaridar The Punch ta fitar ya nuna cewa gwamnoni shida a shiyyar kudu maso yamma sun shirya taron gaggawa kan al'amuran yau da kullum a kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa jaridar ta ruwaito cewa wata majiya daga ganawar ta ce gwamnonin sun hadu ta yanar gizo sannan kuma sun tattauna batutuwan da suka shafi kasa.

KU KARANTA KUMA: Hotunan yadda Kano ta cika ta batse da manyan mutane yayin da ake bikin bai wa Sarkin Kano sandar mulki

Sunday Igboho: Gwamnonin kudu maso yamma sun gudanar da taron gaggawa
Gwamnonin kudu maso yamma sun gudanar da taron gaggawa Hoto: APC
Asali: Facebook

A cewar rahoton, samamen da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suka kai gidan dan fafutukar kasar Yarbawa da ke Ibadan, Sunday Adeyemo, wanda ake kira Sunday Igboho na daga cikin abubuwan da aka tattauna.

Gwamnonin Kudu maso Yamma na iya sanya baki a batun Sunday Igboho

An ruwaito majiyar ta ce:

“Suna ganawa amma babu wanda ya tabbatar da ko saboda Igboho ne. Akwai dalilai da yawa da gwamnoni za su iya haduwa (a kai) musamman ta fuskar mawuyacin halin da ake ciki (a kasar)."

An tattaro cewa gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Rotimi Akeredolu (Ondo), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Kayode Fayemi (Ekiti), Dapo Abiodun (Ogun), Gboyega Oyetola (Osun) da Seyi Makinde (Oyo).

KU KARANTA KUMA: APC ta yanke hukuncin karshe kan Yari da Marafa, ta ce lallai Matawalle ne jagoranta a Zamfara

Taron ya kasance karkashin jagorancin Akeredolu, wanda shine shugaban kungiyar gwamnoni a shiyyar.

Luguden wuta yaran Igboho suka fara mana da muka je bincike, DSS

A wani labarin, jami'an tsaro na farin kaya sun yi ikirarin cewa wasu maza da suke tsammanin masu tsaron Sunday Igboho ne sun yi musayar wuta da jami'ai a yayin samamen da suka kai gidan mai assasa samar da kasar Yarabawa a Ibadan da safiyar Alhamis.

Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis bayan kama mutum 13 a gidan Igboho, Channels TV ta ruwaito.

Kamar yadda Afunanya ya sanar, samamen ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu na cewa ana tara makamai a gidan Igboho, lamarin da yasa ake samun rashin zaman lafiya a yankin kudu maso yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel