PDP na cikin matsala yayin da APC ke zawarcin gwamnan Bayelsa Diri

PDP na cikin matsala yayin da APC ke zawarcin gwamnan Bayelsa Diri

  • Shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ya bukaci Gwamna Douye Diri da ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar
  • Wasu mambobin jam’iyyar PDP ciki har da gwamnan Kuros Ribas, Ben Ayade da takwaransa na jihar Zamfara, Bello Matawalle, sun sauya sheka zuwa APC
  • Diri ya zama gwamnan jihar Bayelsa bayan Kotun Koli ta kori zababben gwamnan waccan lokacin kuma jigon APC

Alamu na nuna cewa jihar Bayelsa na iya bin hanyar jihohin Kuros Riba da Zamfara idan har tayin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi wa Gwamna Douye Diri ya cimma nasara.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa APC na neman Diri ya yi koyi da takwarorinsa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sannan ya sauya sheka zuwa APC ba tare da wani bata lokaci ba.

KU KARANTA KUMA: APC ta yanke hukuncin karshe kan Yari da Marafa, ta ce lallai Matawalle ne jagoranta a Zamfara

PDP na cikin matsala yayin da APC ke zawarcin gwamnan Bayelsa Diri
APC ta nemi gwamnan Bayelsa Diri ya fice daga PDP Hoto: APC
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa jam'iyyar ta kuma bukaci dukkan shugabanninta a jihar wadanda suka tsallaka jam'iyyar PDP a bisa kuskure da su canja shawararsu sannan suyi amfani da damar sauye-sauyen sheka da ake yi daga jam'iyyar a duk fadin kasar sannan su dawo jam'iyyar mai mulki.

Daily Independent ta kuma ruwaito cewa masu ruwa da tsaki na APC a karamar hukumar Ekeremor na jihar sun yi wa Diri da sauran jiga-jigan PDP kwantan bauna yayin ganawa a Yenagoa, babban birnin jihar, a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Bana goyon bayan wani dan arewa ya shugabanci kasa a 2023 - Shettima

APC ta shirye mulki a jihar Bayelsa

Fred Akamu ne ya gabatar da kudirin neman amincewar kuma ya samu goyon bayan Nicodemus Anthony, memba a kwamitin zartarwa na jam'iyyar a karamar hukumar.

PDP ta dumfari 'Kotun Allah ya isa', ta na so a tunbuke Gwamnan Imo, Uzodinma

A wani labarin, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP, ta je kotun koli da sabon roko, ta na neman a tsige gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma daga kan mulki.

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto cewa ana sa rai kotun koli za ta sa ranar da za a saurari shari’ar.

Lauyan da ya tsaya wa PDP a kotun kolin kasar, Phillips Umeadi, ya gabatar da wasu sababbin takardu da suka bukaci Alkalan babban kotun su zauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng