PDP ta dumfari 'Kotun Allah ya isa', ta na so a tunbuke Gwamnan Imo, Uzodinma

PDP ta dumfari 'Kotun Allah ya isa', ta na so a tunbuke Gwamnan Imo, Uzodinma

  • Jam’iyyar PDP mai hamayya ta na so a tsige Gwamnan jihar Imo a kotun koli
  • Lauyan da yake kare PDP ya bukaci a sa rana domin a saurari wannan shari’a
  • PDP ta na ikirarin babu Jam’iyyar da ta ba Hope Uzodinma tikiti a zaben 2019

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP, ta je kotun koli da sabon roko, ta na neman a tsige gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma daga kan mulki.

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto cewa ana sa rai kotun koli za ta sa ranar da za a saurari shari’ar.

Lauyan da ya tsaya wa PDP a kotun kolin kasar, Phillips Umeadi, ya gabatar da wasu sababbin takardu da suka bukaci Alkalan babban kotun su zauna.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta na tona wa kan ta asiri a Jihar Imo

The Nation ta ce abin da ake jira shi ne mataimakin magatakarda (mai kula da sha’anin kara) na kotun, ya tuntubi Alkalin Alkalai domin a sa ranar zama.

Rahotanni sun bayyana cewa ana rokon kotun kolin ta janye hukuncin da ta yi na tsige Emeka Ihedioha daga kujerar gwamna, bayan ya ci zabe a PDP.

Karar da Lauyan PDP ya kai gaban kotu

Wadanda za su gabatar da lauyoyi a kotu a kan karar mai lamba SC/1384/2019, sun hada da Uche Nwosu, jam’iyyar APP, Uche Nnadi da hukumar INEC.

Jam’iyyar PDP ta na ikirarin kotu ta yi kuskure da ta ayyana ‘dan takarar APC, Hope Uzodinma, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Imo na 2019.

PDP ta ce bai dace Sanata Uzodinma ya zama gwamna ba tun da an hana Uche Nwosu shiga zabe saboda ya shiga takara a karkashin jam’iyyun APC da AA.

KU KARANTA: Kwankwaso ya zauna da kusoshin APC, ya na tunanin ficewa daga PDP

Hope Uzodinma
Buhari da APC sun kamfe Imo Hotto: www.tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Lauyan PDP ya na so kotu ta zartar da hukunci cewa da jam’iyyar AA da kuma APC duk ba su da ‘dan takara a zaben saboda rikicin da Nwosu ya jawo.

Haka zalika lauyan jam’iyyar hamayyar ya na so kotu ta zartar da cewa Hope Uzodinma bai da takara, da sunan cewa babu jam’iyyar da ta tsaida shi.

A dalilin wannan PDP ta ke so a karbe takardar shaidar lashe zaben da INEC ta ba Uzodinma, a ba Emeka Ihedioha, wanda ya fi kowa kuri’u a zaben 2019.

Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta dauko hayar wasu zakakuran Lauyoyi biyar da za su shigar da Gwamna Bello Matawalle kotu saboda ya sauya-sheka.

Akwai yiwuwar a koma kotu da Bello Matawalle, wanda dama kotu ce ta ba shi nasara a 2019

Asali: Legit.ng

Online view pixel