Mutum 9 'yan gida daya sun sheka lahira bayan cin abinci mai guba a Zamfara

Mutum 9 'yan gida daya sun sheka lahira bayan cin abinci mai guba a Zamfara

  • Kauyen Jangeme dake jihar Zamfara sun shiga dimuwa bayan mutum 9 'yan gida daya sun mutu a rana daya
  • An gano cewa babbar 'ya'yarsu ce tayi musu Tuwon dawa da gari mai guba duk a cikin rashin sani kuma suka ci
  • Yaro daya ya fara mutuwa, uku suka bi bayanshi, wasu ukun suka sake cewa ga garinku yayin da sauran suka rasu duk a rana daya

Tashin hankali ya fada kauyen Jangeme dake karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara lokacin da wasu 'yan gida daya suka sheka lahira bayan cin guba da suka yi a abinci.

Wani kawun mamatan mai suna Abdullahi Bello ya sanar da Daily Trust cewa yaran sun mutu ne bayan 'yar uwarsu da ta kawo musu ziyara daga gidan mijinta ta yi musu Tuwon dawa.

KU KARANTA: Wurin kwadayi: Da tallafin maƙuden kudade aka yaudari Kanu har aka damke shi

Mutum 9 'yan gida daya sun sheka lahira bayan cin abinci mai guba a Zamfara
Mutum 9 'yan gida daya sun sheka lahira bayan cin abinci mai guba a Zamfara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Majalisar Igbo ta duniya: Sace Nnamdi Kanu aka yi, an tozarta shi fiye da 'yan Boko Haram

Bello ya ce: "Yayin da ta zo gida, ta debo dawa daga rumbu kuma ta kai nika. Wani beran masar da ake kiwo a gidan ya mutu bayan ya ci garin tun kafin ta fara yin tuwon.

"Babu wanda ya gano cewa akwai guba a garin ko batan da beran masar din ya mutu. Ta yi girkin kuma yaran sun ci. Bayan sa'o'i kadan yaro daya ya mutu.

"Daga nan muka kwashi yaran muka mika su asibiti a Gusau inda wasu biyu suka mutu. bayan mun kwashi gawarsu muna birnesu ne aka kira mu cewa wasu uku sun mutu, ciki har da wacce tayi girkin. A takaice dai 'ya'ya takwas tare da mahaifiyarsu suka mutu."

A yayin da aka kai ziyara asibitin Yariman Bakura dake Gusau, Daily Trust ta ga yaro daya daga cikin wadanda suka ci tuwon rai a hannun Allah.

"Tabbas likitoci sun tabbatar da cewa lamarin ya fara ne bayan sun ci abinci mai guba," mai magana da yawun hukumar asibitin, Awwal Usman Ruwan Dorawa ya sanar.

Ya ce likitocin sun yi kokarin ceto rayukan yaran amma matasalar ita ce ba a mika su asibiti da wuri ba.

A wani labari na daban, Kingsley Kanu, dan uwan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB ya ce an kama dan uwansa a kasar Kenya.

Gwamnatin tarayya ta yi shiru kuma bata sanar da inda ta kama Kanu ba, lamarin da yasa ake ta cece-kuce, Daily Trust ta ruwaito.

Amma a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, Kingsley ya ce hukumomin kasar Kenya sun kama dan uwanshi har sai da hukumomin tsaro na Najeriya suka je suka taso keyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel