Da Ɗuminsa: Gwamna Zulum Ya Shilla Ƙasar Nijar, Ya Sa Labule da Shugaba Bazoum
- Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno, ya kai ziyara ƙasar Nijar, inda ya amsa gayyatar da aka masa
- Gwamnan ya gana da shugaban ƙasar Nijar, Muhammadu Bazoum, da gwamnan Diffa, Isa Lameen
- An gudanar da wannan taro ne a garin Diffa, inda shugabannin suka tattauna kan yadda za'a maida yan gudun hijira
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum, yanzun haka yana ƙasar Nijar bisa amsa gayyatar shugaban ƙasa, Muhammad Bazoum.
Shugaba Bazoum ya karɓi bakuncin gwamna Zulum tare da tawagarsa da suka haɗa da Kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkareem Lawan da Sanata Abubakar Kyari, inda suka shiga taron sirri a garin Diffa.
KARANTA ANAN: Wasu Fusatattun Mata da Ƙananan Yara Sun Toshe Hanyar Sokoto-Gusau
Taron ya maida hankali ne kan yan gudun hijira, waɗanda suka baro ƙauyukansu daga sassa daban-dabn na jihar Borno tun shekarar 2014, saboda yawaitar hare-haren yan Boko Haram.
An fara taron ne jim kaɗan bayan gwamna Zulum da takwaransa na Diffa, Gwamna Lameen sun tarbi shugaba Bazoum a filin tashi da saukar jiragen sama na Tanja Momadou dake garin Diffa.
Garin Diffa na kusa da yankuna da dama na arewacin jihar Borno, yayin da garuruwa da dama a Borno suka haɗa iyaka da garin Diffa.
Zulum ya yi jawabi ga manema labarai bayan taron
Gwamna Zulum ya zanta da manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga taron. Hakan na ƙunshe ne a wani rubutu da gwamnan yayi a shafinsa na facebook.
Gwamnan yace: "Mun cimma abubuwa da dama a taron, Mun ɗauki wasu matakai da suka haɗa da maida yan asalin jihar Borno zuwa garuruwansu."
"Waɗannan mutanen sun ɗauki tsawon shekaru 6 a Nijar, Amma sabida cigaban da muka samu a ɓangaren tsaro, yanzun mutanen sun ƙosa su koma gidajensu."
"Zamu yi iyakar bakin ƙoƙarin mu wajen ganin mutanen mu sun koma ƙauyukansu cikin ƙoashin lafiya."
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Majalisa Sun Yi Fatali da Buƙatar Ɗage Dokar Hana Twitter
Waɗanda suka mara wa gwamna Zulum baya zuwa Nijar sun haɗa da, Sanata mai wakiltar Borno ta arewa, Abubakar Kyari, kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarin Lawan da kuma wasu ƙusoshin gwamnatin jihar.
A wani labarin kuma Matawalle Ya Yi Magana Kan Kisan Ɗan Majalisar Jiharsa, Ya Bayyana Alhininsa
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalli, ya yi jimamin kisan da aka yiwa ɗan majalisar dokokin jiharsa, Hon. G. Ahmed.
Gwamnan yayi ta'aziyya ga iyalan mamacin tare da addu'ar neman samun rahamar ubangiji.
Asali: Legit.ng