Wasu Fusatattun Mata da Ƙananan Yara Sun Toshe Hanyar Sokoto-Gusau

Wasu Fusatattun Mata da Ƙananan Yara Sun Toshe Hanyar Sokoto-Gusau

  • Yan ƙauyen Garmar Hannu ƙaramar hukumar Maru, sun toshe hanyar Sokoto Gusau saboda yawaitar harin yan bindiga
  • Mutanen wanda mafi yawancin su mata ne da ƙananan yara sun bayyana cewa sun yi haka ne domin jan hankalin gwamnati
  • A halin yanzun fasinjoji da yawa sun taru yayin da suke jiran waɗanda suka toshe hanyar su hakura

Mutanen ƙauyen Garmar Hannu, ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamafara sun toshe hanyar Sokoto-Gusau ranar Alhamis, suna zanga-zanga kan yawan kashe mutanen su da yan bindiga ke yi, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Majalisa Sun Yi Fatali da Buƙatar Ɗage Dokar Hana Twitter

Hanyar Sokoto-Gusau ita ce hanyar da mutane suka fi bi idan zasu je Sokoto, Kebbi, Zamfara da sauran sassan ƙasar nan da suka haɗa da Kaduna, Kano, Abuja, Lagos da Patakwal.

Mutanen ƙauyen waɗanda mafi yawancin su mata ne da ƙananan yara sun toshe hanyar ne a kusa da Tashar Abu, ƙaramar hukumar Bungudu, inda suka hana matafiya wucewa.

Mutane sun toshe hanyar Sokoto-Gusau
Wasu Fusatattun Mata da Ƙananan Yara Sun Toshe Hanyar Sokoto-Gusau Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin, Umar Yusuf, ya shaidawa manema labarai cewa basu da wani zaɓi ne da ya wuce su fito zanga-zanga, tun da an kasa magance musu waɗannan yan ta'addan.

Yusuf, yace: "Ana kashe mutanen ƙauyen Garmar Hannu da kuma sace su kusan kullum, sabida haka ne suka fito ko Allah zai sa su jawo hankalin gwamnatin jihar."

Wani fasinja da lamarin ya shafa, Ayomide Adeyemo, yace ya taho ne daga Lagos zuwa Anka, ya koka da cewa an tare shi anan na tsawon wasu awanni.

KARANTA ANAN: Matawalle Ya Yi Magana Kan Kisan Ɗan Majalisar Jiharsa, Ya Bayyana Alhininsa

Mutanen ƙauyen Bingi sun yi makamancin haka a baya

Idan zaku iaya tunawa, a makon da ya gabata ne mutanen ƙauyen Bingi ƙaramar hukumar Maru, sun yi makamancin wannan zanga-zanga.

A yayin wannan zanga-zangar, mutanen ƙauyen sun tara gomman motoci yayin da ɗaruruwan fasinjoji suka taru saboda toshe hanyar da aka yi.

A wani labarin kuma Ba Zamu Huta ba Har Sai Mun Tabbatar da Yan Najeriya Na Bacci da Ido Biyu, IGP

IGP Usman Baba, ya bayyana wa yan majalisar wakilai cewa hukumarsa na aiki ba dare ba rana domin bada tsaro ga yan Najeriya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Baba ya faɗi haka ne yayin da ya bayyana gaban kwamitin kula da ayyukan hukumar yan sanda ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel