Dalla-dalla: Da na "hannun daman" Nnamdi Kanu aka hada kai aka kama shi

Dalla-dalla: Da na "hannun daman" Nnamdi Kanu aka hada kai aka kama shi

  • Wata kungiyar kare 'yancin dan Adam da bin dokoki ta ce da makusantan Nnamdi Kanu aka hada kai aka kama shi
  • Kamar yadda kungiyar ta tabbatar, akwai wata matsala dake tsakanin Kanu da wasu 'yan kabilarsa wanda yasa suka bada hadin kai
  • Kungiyar tace da farko anyi zaton cewa matsala ce tsakanin Kanu da jami'an hukumar shige da fice amma sai jami'an Najeriya suka kama shi

Wata kungiya mai suna International Society for Civil Liberties and Rule of Law, ta ce "makusanta kuma shakikan Nnamdi Kanu ne suka saka masa tarko a kan wata matsala dake tsakaninsu."

Kungiyar ta ce kamen da aka yi wa Kanu a filin jirgin sama da farko an yi zaton karamin lamari ne tsakaninsa da jami'an hukumar shige da fice, wanda daga bisani ya bayyana cewa da gangan ne kuma daga bisani aka saka jami'an diflomasiyya na Najeriya.

KU KARANTA: Labarin biloniya mai shekara 60 wanda ya tara sama da N380b kuma yake yawo a keke

Dalla-dalla: Da na "hannun daman" Nnamdi Kanu aka hada kai aka kama shi
Dalla-dalla: Da na "hannun daman" Nnamdi Kanu aka hada kai aka kama shi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan iyalan Buhari da suka dira birnin London don yayen Hanan daga makaranta

A yayin bada bayani game da yadda aka kama Kanu, takardar da shugabannin kungiyar Emeka Umeagbalasi, Obianuju Igboeli, da Chidimma Udegbunam, ta ce, "an janyo hankalon jami'an diflomasiyya na Najeriya da kuma jami'an tsaro a Nairobi, babban birnin kasar.

"A ranar Lahadi, 27 ga watan Yunin 2021 an mika shi hannun jami'an tsaro da kuma jami'an diflomasiyya bayan sun bada shaidar cewa ana nemansa a Najeriya domin a cigaba da shari'ar da ya tsere ana yi," Kungiyar tayi ikirarin.

Kungiyar 'yancin dan Adam din tace abin jinjinawa ne ta yadda aka dawo da Nnamdi Kanu Najeriya ba tare da an sunkumo shi a jaka ba, Daily Trust ta ruwaito.

Takardar ta kara da cewa: "Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, an kama shi a daren Asabar 26 ga watan Yunin 2021 a Kenya, kasar dake cikin kungiyar gamayyar Afrika.

"Ya ziyarci Isra'ila bayan ya je Jamus sannan ya doshi kasar Kenya inda aka cafke shi a ranar Asabar, 26 ga watan Yunin 2021.

“Wasu makusantan shi ne suka saka masa tarko kuma 'yan yarensa ne suka hada komai."

A wani labari na daban, an janyo hankalin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, zuwa wata kasa a Afrika ne bayan an dauka alkwarin bashi tallafin miliyoyin daloli, jaridar TheCable ta gano hakan.

Shugaban IPOB wanda ke fuskantar wasu tuhuma da suka hada da cin amanar kasa bayan gangamin son rabe kasar Najeriya, ya tsallake belinsa da aka bada a 2017 bayan gurfana da yayi a gaban kotu.

Majiyoyin tsaro sun sanar da TheCable cewa an fara shirin kama Kanu tare da dawowa da shi kasar Najeriya da dadewa, amma sai ranar 27 ga watan Yuni aka samu nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel