Yanzu Yanzu: Rundunar sojoji ta kashe ‘yan ta’adda 73, ta ceto mutum 55 a Borno

Yanzu Yanzu: Rundunar sojoji ta kashe ‘yan ta’adda 73, ta ceto mutum 55 a Borno

  • Rundunar sojojin Najeriya ta halaka wasu manyan ‘yan ta’adda a jihar Borno
  • Hakanan, sojoji sun kubutar da mutane 55 daga hannun ‘yan ta’addan a tsakanin 18-30 ga watan Yuni a cewar hedikwatar tsaro
  • Haka kuma, an kwato bindigogin AK 47 guda 44, PKT 2, bindigogin harbo jirgin sama guda 7, manyan bindigogi 7, alburusai masu yawa iri daban-daban daga hannun su

Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce sojojin Operation HADIN KAI sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram 73 tare da ceto mutum 55 a jihar Borno.

Mukaddashin daraktan labarai na tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a lokacin da yake karin haske kan ayyukan sojoji a duk fadin kasar tsakanin 18-30 ga watan Yuni, 2021.

Ya ce ayyukan sun haifar da ‘ya’ya masu idanu ta bangarori daban-daban a duk fadin kasar, jaridar Leadership ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa sun tabarbare tsakanin Ganduje da hukumar yaki da rashawa ta Kano

Yanzu Yanzu: Rundunar sojoji ta kashe ‘yan ta’adda 73, ta ceto mutum 55 a Borno
Rundunar soji ta yi nasarar halaka 'yan ta'addan Boko Haram masu yawa a Borno Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ya ce sojojin sun gudanar da ayyukan kwanton-bauna, ayyukan kakkaba tare da amsa kiraye-kiraye masu wahala sannan sun dakile hare-haren ta’addanci a wuraren da sojoji suke.

Kakakin hedkwatar tsaron ya ce bangaren rundunar sojin sama na Operation HADIN KAI ya kuma gudanar da jerin ayyukan sa ido kan ayyukan leken asiri da kuma aika sakonni don lalata mafakar ‘yan ta’adda da kuma kayan aikinsu.

Janar Onyeuko ya kara da cewa sojojin na ci gaba da fatattakar wuraren Boko Haram/ ISWAP a duk inda suke gudanar da aikin.

Ya ce a yayin farmakin, an kashe ‘yan ta’adda da dama kuma an kwato kayayyaki da makamai da yawa.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun karbi N20m a matsayin kudin fansa, amma sun ki sako ’yan makarantar Neja

“An kashe ‘yan Boko Haram 73 tare da kwato bindigogin AK 47 44, PKT 2, bindigogin harbo jirgin sama guda 7, manyan motocin da ake girke bindiga a kai 7, alburusai da yawa da kayan tsabtace makamai, kayan sawa, barguna, kayan abinci, motoci, janareto, kayan bama-bamai, rubutun addini da sauran abubuwa a yayin aikin.
"Jimillan wadanda suka tsere daga sansanonin 'yan ta'adda da suka hada da maza manya 15, mata manya 12 da yara 27 sun mika wuya ga sojoji a Darajemel da ke jihar Borno," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, rundunar sama na Operation HADIN KAI, a wasu hare-hare da ta kai ta sama, ta lalata wasu rundunonin kwamandan ‘yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi da ke jihar ta Borno, jaridar The Guardian ma ta ruwaito.

Onyeuko ya ce an kai harin ne kan sansanonin ‘yan ta’adda daban-daban a Sabon Tumbu, Jibularam da Kwalaram a Jihar.

Ya ce an kai harin ne bayan wani rahoton sirri wanda ya nuna cewa wasu manyan kwamandojin ISWAP/Boko Haram suna gudanar da taro a wuraren da aka ambata.

Sojoji sun bankado sharrin ‘Yan Boko Haram, sun yi wa Mayakan ta’adda kwaf-daya

A wani labarin, rundunar Operation Hadin Kai ta yi nasarar kashe wasu daga cikin sojojin kungiyar Boko Haram da na Islamic State West Africa Province watau ISWAP.

Jaridar Punch ta bayyana cewa an hallaka ‘yan ta’addan ne bayan sojojin sama sun taimaka wa dakarun Operation Hadin Kai wajen auka wa ‘yan ta’addan.

Rahoton ya ce ‘yan ta’adda 12 aka kashe a sanadiyyar wannan fito-mu-gama da bangarorin biyu su ka yi a jihar Borno, aka rika musayar wuta da bindigogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel