Abubuwa sun tabarbare tsakanin Ganduje da hukumar yaki da rashawa ta Kano

Abubuwa sun tabarbare tsakanin Ganduje da hukumar yaki da rashawa ta Kano

  • Wata takaddama ta kunno kai tsakanin gwamnatin Ganduje da kuma Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta Jihar Kano (PCACC)
  • Hakan ya biyo bayan binciken da hukumar ke yi kan wasu kwangiloli da aka bai wa wasu iyalan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
  • Sai dai hukumar ta ce hakan babu wata manufa da suke da ita a kan iyalan Gwamnan

Wani rikici ya kunno kai a yanzu haka a Kano tsakanin gwamnatin jihar da shugaban hukumar da ke sauraron korafe-korafen jama'a da yaki da cin hanci da rashawa (PCACC), Muhuyi Magaji Rimin-Gado.

Hakan ya biyo bayan binciken da hukumar ta fara kan kwangilolin da aka ce yana da nasaba da wasu dangin Gwamna Abdullahi Ganduje, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun ce shawarar da hukumar yaki da rashawa ta yanke a kwanan nan na binciko wasu ayyukan da suka hada da Cibiyar Yaki da Cutar Daji da kuma samar da man dizal ya cika da wasu daga cikin dangin gwamnan.

Abubuwa sun tabarbare tsakanin Ganduje da hukumar yaki da rashawa ta Kano
Muhuyi ya tabbatar da binciken da hukumar da yake jagoranta ke gudanarwa Hoto: Aminiya
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Jagoran APC a Zamfara: Yari da Marafa basu yarda da jagorancin Matawalle ba

Rimin-Gado, wanda ya tabbatar da binciken, ya ce hakan babu wata manufa da suke da ita a kan iyalan Gwamnan amma hukumar ba za ta ragawa kowa ba.

Akwai rahoto kan yunkurin da ake zargin Ganduje ya yi na cire Rimin-Gado.

An ce gwamnan na ci gaba da matsin lamba ga Majalisar Jihar don ta bincike shi.

Gabanin binciken da ake zargin yi kan Rimin-Gado, gwamnatin jihar ta tura akawu daga Ofishin Akanta-Janar na jihar don maye gurbin wani matashin jami’i da aka ce dan uwan ​​shugaban PCACC ne.

Kafin maye gurbinsa, jami'in ya yi aiki a matsayin akawun hukumar.

KU KARANTA KUMA: Hanyar da mu ka bi aka taso keyar Nnamdi Kanu bayan shekaru 2 ana nemansa inji Minista

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawar, wanda ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa yana maraba da binciken, ya ki amincewa da shawarar tura sabon akawu zuwa hukumar.

A wani labarin, hukumar Hisbah da ke da alhakin dabbaka tsarin shari’ar musulunci a jihar Kano, ta bada sanarwar haramta amfani da mutum-mutumi wajen tallata kaya.

Tribune ta rahoto hukumar a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, 2021, ta na gargadin teloli, masu shago da ‘yan kasuwa da ke rataya kaya kan mutum-mutumin.

Hisbah ta ja-kunnen masu wannan aiki da cewa dakarunta za su bi shaguna da kasuwanni suna jefar da wadannan mutum-mutumi domin suna kama da gumaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel