Sojoji sun bankado sharrin ‘Yan Boko Haram, sun yi wa Mayakan ta’adda kwaf-daya
- An yi ba-ta-kashi tsakanin Sojojin Najeriya da ‘Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP
- Kakakin Sojan kasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya ce an kashe mutum 12
- Sojojin sama ne su ka taimaka wa sojojin kasa wajen lallasa mayakan ‘yan ta’addan
Rundunar Operation Hadin Kai ta yi nasarar kashe wasu daga cikin sojojin kungiyar Boko Haram da na Islamic State West Africa Province watau ISWAP.
Jaridar Punch ta bayyana cewa an hallaka ‘yan ta’addan ne bayan sojojin sama sun taimaka wa dakarun Operation Hadin Kai wajen auka wa ‘yan ta’addan.
Rahoton ya ce ‘yan ta’adda 12 aka kashe a sanadiyyar wannan fito-mu-gama da bangarorin biyu su ka yi a jihar Borno, aka rika musayar wuta da bindigogi.
KU KARANTA: Halin da aka shiga ya damu jama'a - Jonathan
Mun ci galaba a kan 'Yan ta'adda - Onyema Nwachukwu
Gidan sojan kasan Najeriya a shafinta na Facebook ta ce mayakan ‘yan ta’addan sun yi yunkurin kai hari ga wani sansanin sojoji da ke garin Bula, jihar Borno.
Bayan sojoji sun ci karfin su, dole ta sa ‘yan ta’addan suka hakura da ta’adin na su, suka tsere.
Mai magana da yawun bakin sojojin Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa an rasa sojoji biyu a harin, sannan biyu sun samu rauni.
Jami’in ya yi wa jawabin na ranar Litinin take da: “Operation Hadin Kai: Troops in conjunction with Air Component neutralise BHT/ISWAP terrorists in Borno.”
KU KARANTA: Ba a iya shiga wasu yankuna a Borno - Shehu
Janar Onyema Nwachukwu a jawabin da ya fitar a madadin rundunar sojoji na kasa, ya bayyana cewa jami’an da suka samu rauni suna jinya a asibiti a halin yanzu.
Bayan haka, Nwachukwu ya ce an samu wasu makamai a hannun ‘yan ta’addan, daga ciki akwai mota mai luguden wuta, katuwar bindigar QJC da kuma AK-47.
An samu zaman lafiya a yankin FOB Bula, Borno saboda kokarin da jami’an tsaron su ka yi.
Makonni bayan mutuwar tsohon shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ‘yan ta’addan ISWA sun yi sabon jagora, Ibrahim Al-Hashimiyil Khuraishi.
Kungiyar ISWAP ta yi sulhu da bangaren Boko Haram da su ka yi wa Abubakar Shekau mubaya’a.
Asali: Legit.ng