‘Yan Hisbah sun haramta amfani da mutum-mutumi wajen tallata kaya a fadin jihar Kano

‘Yan Hisbah sun haramta amfani da mutum-mutumi wajen tallata kaya a fadin jihar Kano

  • Dakarun Hisbah za su rushe mutum-mutumi da ake ajiyewa a shaguna a Kano
  • Hukumar ta Hisbah ta ce amfani da gumakan ya sabawa addinin musulunci
  • Sheikh Haruna Ibn Sina ya bada wannan sanarwa, ya ce za su dauki mataki

Hukumar Hisbah da ke da alhakin dabbaka tsarin shari’ar musulunci a jihar Kano, ta bada sanarwar haramt amfani da mutum-mutumi wajen tallata kaya.

Tribune ta rahoto hukumar a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, 2021, ta na gargadin teloli, masu shago da ‘yan kasuwa da ke rataya kaya kan mutum-mutumin.

Hisbah ta ja-kunnen masu wannan aiki da cewa dakarunta za su bi shaguna da kasuwanni suna jefar da wadannan mutum-mutumi domin suna kama da gumaka.

KU KARANTA: Hukumar Hisbah ta kama mata da miji su na satar jarirai

Haka zalika, jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban majalisar da ke kula da hukumar, Sheikh Haroun ibn Sina, ya na bada wannan sanarwar a ranar Laraba.

Hakan ya ci karo da shari'ar musulunci

Sheikh Haroun ibn Sina ya ke cewa shagunan saida kaya da wuraren dinki da suke ajiye wannan dodo sun saba wa shari’ar musulunci da ake bi a jihar ta Kano.

Shehin malamin ya ce hujjar hukumar Hisbah na yin haka shi ne wadannan gumaka da ake ajiye wa wajen kasuwanci suna cusa wa miyagu tunanin banza a ransu.

Sheikh Ibn Sina yake cewa:

“Hukumar Hisbah ta haramta amfani da mutum-mutum a shaguna, gidajen kai da na kasuwa, da wasu wuraren da ake zama a fili.”

KU KARANTA: Mace aka yi amfani da ita, aka taso keyar Nnamdi Kanu Najeriya

Mutum-mutumi
Wani mutum-mutumi a shago
Asali: Getty Images
“Wannan ya saba wa dokar addinin musulunci, shi ne yake jawo tunanin banza a zuciyar wasu mutane, wannan duk ya ci karo da addini.”

Wannan dokar za ta fara aiki - Hisbah

“Mun kasa jihar Kano zuwa biyar, domin a dabbaka wannan haramci a fadin jihar.”

Hisbah ta ce za ta shiga wayar da kan al’umma a kan yadda addinin musulunci ya ke kyamar irin wannan abubuwa, sannan a hukunta wadanda suka saba wannan doka.

Kwanakin baya kun ji cewa Hukumar Hisbah ta jihar Kano kafa wani kwamiti domin binciken wani jami'in ta da ake zargi da kwanciya da wata matar aure a dakin otel.

Rahotanni sun ce an samu wannan mutumi da rashin gaskiya, a karshe aka kora shi daga aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel