Ni Ba Mai Cin Hanci da Rashawa Bane, Kowa Ya Sani, Buhari ya Jaddada Martabarsa

Ni Ba Mai Cin Hanci da Rashawa Bane, Kowa Ya Sani, Buhari ya Jaddada Martabarsa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa,shi ba dan rashawa bane kuma ba a taba zarginsa da rashawa ba
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake bayyana cewa matsalolin Najeriya a jikin 'yan Najeriya suke ba a addini ko kabila ba
  • Ya godewa wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen ganin ya hau karagar mulki a zaben 2015

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi alfaharin cewa, a tsawon tarihin rayuwarsa ta aiki da gudanar da mulki, babu wanda ya taba zarginsa da cin hanci da rashawa

Shugaban ya bayyana haka ne yayin da yake bayanin matsalolin da Najeriya ke ciki da kuma wadanda suka yi mai yiwuwa wajen jefa kasar a halin da take ciki.

Ya bayyana cewa, 'yan Najeriya su ne matsalar Najeriya ba wai bambancin addini, al'ada ko bangare ba, ya kuma bayyana yadda ya samu goyon baya daga addinai da kabilu daban-daban a Najeriya.

KARANTA WANNAN: Wata Kungiyar Igbo Ta Bukaci Kasar Burtaniya Ta Sa Baki Kan Kame Nnamdi Kanu

Ni Ba Mai Cin Hanci da Rashawa Bane, Kowa Ya Sani, Buhari Jaddada Matsayinsa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake ranstuwar kama aiki | Hoto: voanews.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da mashawarci na musamman ga shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar, wacce Legit.ng Hausa ta samo, Buhari ya bayyana martabarsa ya kuma godewa Allah cewa shi ba mai cin hanci da rashawa bane.

A cewar sanarwar, Buhari ya ce:

“Na gode wa Allah cewa tsawon shekaru, ba za su iya zargi na da cin hanci da rashawa ba. Kuma na rike matsayin komai; Gwamna, Ministan Albarkatun Man Fetur, Shugaba a kasa, Shugaban kasa, kuma a wa’adi na na biyu."

Ya kuma godewa wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen tabbatar ya samu adalci a zaben da ya kawo shi shugaban Najeriya, yana mai cewa:

"Na gode muku cewa babu wanda ya tilasta muku, amma kun taru, kun yi amfani da karfinku, lokacinku, da dukiyoyinku, na gode sosai. Ina baku tabbacin, tarihi ba zai manta daku ba.”

KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Wasu Daga Cikin Daliban Islamiyya da Aka Sace a Jihar Neja Sun Tsere

Wata Kungiyar Igbo Ta Bukaci Kasar Burtaniya Ta Sa Baki Kan Kame Nnamdi Kanu

A wani labarin, Shugabannin kungiyar Ijaw National Congress (INC) sun gargadi Gwamnatin Tarayya da ta dauki barazanar da kungiyar Tsagerun Neja Delta (NDA) ta fitar da gaske, jaridar Sun ta ruwaito.

Ta kuma bayyana cewa babu wata yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya yayin taronta na kwanan nan wanda zai dakatar da tashin hankali daga mutanen yankin.

NDA a karshen mako ta sanar da shirin Operation Humble wanda ta ce zai gurgunta tattalin arzikin Najeriya bisa gazawar Gwamnatin Tarayya na magance matsalar rashin ci gaba a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel