Kabilar Ijaw Ta Gargadi Buhari Kan Tamkawa Tsagerun Neja Delta da Ya Yi

Kabilar Ijaw Ta Gargadi Buhari Kan Tamkawa Tsagerun Neja Delta da Ya Yi

  • Kungiyar Ijaw National Congress ta gargadi shugaba Buhari kan batunn hare- haren tsagerun Neja Delta
  • Kungiyar ta ce babu wata yarjejeniya dake tsakanin shugaban kasan da kabilar yankin kan matsalolinsu
  • A bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da barazanar ta su, tare da bayyana matsayarsa

Shugabannin kungiyar Ijaw National Congress (INC) sun gargadi Gwamnatin Tarayya da ta dauki barazanar da kungiyar Tsagerun Neja Delta (NDA) ta fitar da gaske, jaridar Sun ta ruwaito.

Ta kuma bayyana cewa babu wata yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya yayin taronta na kwanan nan wanda zai dakatar da tashin hankali daga mutanen yankin.

NDA a karshen mako ta sanar da shirin Operation Humble wanda ta ce zai gurgunta tattalin arzikin Najeriya bisa gazawar Gwamnatin Tarayya na magance matsalar rashin ci gaba a yankin.

KARANTA WANNAN: Bayan Harbe Mata Mai Juna Biyu da Sace Mijinta, 'Yan Bindiga Sun Nemi Fansa N3Om

Kabilar Ijaw Ta Gargadi Buhari Kan Tamkawa Tsagerun Neja Delta da Ya Yi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Fadar shugaban kasa ta ce, barazanar ta NDA na baya-bayan nan ba ta da wani muhimmanci saboda ta gana da shugabannin INC kuma ta amsa batutuwan da aka gabatar musamman kan sake fasali da kuma rantsar da kwamitin Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).

Sai dai, shugaban INC, Farfesa Benjamin Okaba a cikin martaninsa game da bayanin da fadar shugaban kasar ta yi, ya ce tawagar ba ta yi wani taron tattaunawa ba.

A cewarsa, sauraran shugaban bayan sun gabatar da bukatunsu guda 10 ba yana nufin kungiyar ta yarda da abin da ya fada bane.

Ya ce dalilin da ya sa shugabannin Ijaw suka je Abuja shi ne don kaucewa ayyuka irin wanda NDA kan iya yi.

Buhari ya yi martani kan barazanar da Niger Delta Avengers ta yi na gurgunta tattalin arzikin Nigeria

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana barazanar da kugiyar Niger Delta Avengers ta yi na fara kaiwa rijiyoyin man fetur da wasu kayyayakin hari a yankin kudu maso kudu a matsayin abin da 'ba a bukatarsa' a yanzu, The Cable ta ruwaito.

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, a shafinsa na Facebook ya ce shugaban kasar ya tattauna da shugabanin kungiyar yan Niger Delta da Ijaw, INC, a fadarsa a ranar Juma'a.

Sun ce yankin na kudu maso kudu shine mafi koma baya wurin cigaba a kasar kuma ba a yin wani yunkurin samar da bukatunsu.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Asabar, ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta dauka mata.

KARANTA WANNAN: PDP Ta Ja Kunnen Gwamna Matawalle Kan Komawa APC, Ta Ce Za Ta Kwace Kujerarsa

Kungiyar ESN Ta Kashe Bokanta Bisa Yin Tsafin da Bai Yi Tasiri Kan ’Yan Sanda Ba

A wani labarin na daban, Mambobin haramtacciyar kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) sun harbe wani mutum, mai suna Paschal Okeke, wanda ke kera “layar cin nasara” ga kungiyar saboda gazawar layarsa wajen karesu na tsawon shekaru, in ji ‘yan sanda a jihar Imo.

Wata sanarwa daga ‘yan sanda ta ce, kungiyar ta fusata da cewa layar, wanda ya kamata ta sa ba za a iya cin nasara a kansu ba kuma su tsere wa farmakin jami’an tsaro ba ta yi wani tasiri ba.

‘Yan sanda sun ce kisan ya biyo bayan samun nasarar 'yan sanda na kai samame a maboyar kungiyar da kuma ragargazar mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel