Kwastam ta kama tabar wiwi ta fiye da Naira Miliyan 91 ɓoye a motar yashi a Legas

Kwastam ta kama tabar wiwi ta fiye da Naira Miliyan 91 ɓoye a motar yashi a Legas

  • Wata motar yashi makare da tabar wiwi ta shiga a Jihar Lagos
  • An kiyasta kudin tabar kusan fiye da kimanin naira miliyan 91
  • An boye tabar da kai sinki dubu uku cikin buhu 41 a tsakiyar yashi cikin wata tifa

Jami'an hukumar Kwastam reshen Seme ta bankado sinki 3,186 na tabar wiwi da aka ɓoye a cikin tifa dauke da yashi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Sinkin wiwin, wanda aka ɗaure a akalla buhu 41 a cikin tifa an kama ta ne a titin Seme-Badagry, an ƙiyasta kudin ta zai kai kimanin naira miliyan 91,488,977.

Kwastam ta kama tabar wiwi ta fiye da Naira Miliyan 91 a Legas
Kwastam ta kama tabar wiwi ta fiye da Naira Miliyan 91 ɓoye a motar yashi a Legas. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Mafarauta sun ɗirka wa mai garkuwa harsashi ya mutu yayin da yazo karɓar kuɗin fansa

The Cable ta ruwaito cewa Abdullahi Hussain, mai magana da yawun Kwastam shiyyar Seme, a wata sanarwa ranar Laraba, ya ce an kama tifar da safiyar Talata, bayan bayanan sirri da suka samu.

A rahoton NAN, an binciki motar, kuma an gano buhi 41 ɗauke da sinki 3,186 na tabar wiwi, da shaidar da biyan kuɗi kimanin N91,488,977.

Abdullahi ya kara da cewa Bello Jibo, shugaban shiyyar Seme na Kwastam, ya yaba da aikin tare da karfafa mu su gwiwa wajen zakulo ayyukan bata gari a fadin ƙasa.

KU KARANTA: 'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023

Ya kuma roki jami'an da su hada kai da mutanen gari, don samun goyon bayan su wajen gudanar da aikin su.

Kotu ta yanke wa direban masu garkuwa da mutane hukuncin kisa ta hanyar harbi

Wata babban kotu a Jihar Bayelsa, da ke zamanta a Yenagoa, ta yanke wa wani matashi dan shekara 39, Charles Nikson, hukuncin kisa ta hanyar harbi, The Punch ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kama shi da laifin hada kai a garkuwar da a kayi da Alex Iliemokumo da Vivian Okoye, matar wani mashahurin dan kasuwa kuma ma'aikacin lafiya a Jihar Bayelsa a cikin watan Nuwambar 2020.

Okeye, matar Obinna Okeye, wanda aka fi sani da Blessed Obaino mamallakin shagunan A-Z Electronics a sassa mabambanta na Yenagoa, da kuma ma'aikacin lafiya da aka fi sani da Alex Ogregade Ileimokumo daga yankin Igbedi na karamar hukumar Southern Ijaw, an ceto su bayan an yi musayar wuta da jami'an Operation Puff Adder.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: