Hisbah ta kama matasa a Kano kan zarginsu da ayyukan badala, Kwamanda

Hisbah ta kama matasa a Kano kan zarginsu da ayyukan badala, Kwamanda

  • Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta damke matasa 40 bisa ayyukan badala a jihar
  • An kama su suna ayyukan da suka hada da lalata, siyar da tabar wiwi da kwaroron roba
  • Hukumar tace za ta saki wadanda aka kama a karon farko, sauran kuwa za a kaisu kotu

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wasu matasa 40 a kan zarginsu da ayyukan badala a cikin birnin Kano.

Kwamandan Hisbah, Dr Harun Ibn-Sina, ya bayyana hakan a ranar Talata a wata takarda da Lawal Ibrahim, mai magana da yawun hukumar a jihar Kano ya fitar.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, Ibn-Sina yace daga cikin wadanda ake zargin 40 da aka kama, 12 daga ciki duk maza ne.

KU KARANTA: Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure

Hisbah ta kama matasa a Kano kan zarginsu da ayyukan badala, Kwamanda
Hisbah ta kama matasa a Kano kan zarginsu da ayyukan badala, Kwamanda. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita

"An kama wadanda ake zargi tsakanin 27 zuwa 28 ga watan Yuni wurin karfe 10 na dare zuwa tsakar dare a wani samame na musamman da suka kai Bur-burwa, karamar hukumar Albasu inda karuwai ke tattaruwa suna aikata badala da siyar da wiwi da kororon roba.

"An kama wasu wadanda ake zargi a wuraren titin jirgin kasa, Ja'en, Zoo Road da sauransu," yace.

Kamar yadda Pulse ta wallafa, Ibn-Sina yace za a tantance wadanda aka kama, wadanda wannan ne karonsu na farko, za a mika su ga iyayensu yayin da sauran za a gurfanar dasu a gaban kotu.

Kwamandan yayi kira ga matasa da su dinga tsoron Allah tare da gujewa miyagun dabi'u.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa "ayyukan badala" an haramta su karkashin dokokin Shari'a a jihar Kano.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta musanta rahoto dake yawo na cewa ta tura jami'an tsaro domin musgunawa dalibai masu zanga-zanga a kwalejin ilimi, wanda hakan ya janyo ajalin dalibi daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan yana zuwa ne bayan sa'o'i kadan da jami'an tsaro suka harbe wani dalibi daga cikin daruruwan dake zanga-zanga kan karin kudin makaranta.

A wani bayani ga manema labarai da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan yayi, ya ce gwamnatin jihar Kaduna tana jiran bayanai domin su bata damar gano abinda ke kunshe a cikin rikicin da ya barke a Gidan Waya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel