Wurin kwadayi: Da tallafin maƙuden kudade aka yaudari Kanu har aka damke shi

Wurin kwadayi: Da tallafin maƙuden kudade aka yaudari Kanu har aka damke shi

  • Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa ba a Ingila, Brazil ko a Czech aka damke Nnamdi Kanu ba
  • An yaudaresa da cewa za a baiwa kungiyar IPOB tallafin miliyoyin daloli inda ya garzaya karba
  • Kanu bai sanar da mukarrabansa batun kudin ba, ya je karba baki alaikum ba tare da saninsu ba

An janyo hankalin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, zuwa wata kasa a Afrika ne bayan an dauka alkwarin bashi tallafin miliyoyin daloli, jaridar TheCable ta gano hakan.

Shugaban IPOB wanda ke fuskantar wasu tuhuma da suka hada da cin amanar kasa bayan gangamin son rabe kasar Najeriya, ya tsallake belinsa da aka bada a 2017 bayan gurfana da yayi a gaban kotu.

Majiyoyin tsaro sun sanar da TheCable cewa an fara shirin kama Kanu tare da dawowa da shi kasar Najeriya da dadewa, amma sai ranar 27 ga watan Yuni aka samu nasara.

"Ba a Ingila, Brazil ko jamhuriyar Czech aka kama shi ba kamar yadda ake yadawa," majiyar tace.

KU KARANTA: Dattijuwa mai shekaru 55 tayi haihuwar farko, mijinta ya tsere, ta samu kyautar N400K

Wurin kwadayi: Da tallafin maƙuden kudade aka yaudari Kanu zuwa Afrika
Wurin kwadayi: Da tallafin maƙuden kudade aka yaudari Kanu zuwa Afrika. Hoto daga @thecableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Legas bayan Sunday Igboho ya sha alwashin gangami a jihar

Gwamnatin Najeriya bata sanar da sunan kasar da ta kama Kanu ba, sai dai Abubakar Malami, ministan shari'a na tarayya ya ce an kama shi kuma an dawo da shi Najeriya.

Sai dai wata jaridar yanar gizo mai suna The Will tace an kama Kanu a kasar Ethiopia inda ya dade yana rayuwa.

Jaridar ThisDay kuwa kai tsaye tace an kama Kanu a babban birnin Ethiopia, Addis Ababa.

TheCable ta gano cewa an kai ga Kanu bayan an yi amfani da wasu mambobin IPOB da aka kama bayan gagarumin samamen da sojoji suka yi a yankin kudu maso gabas.

Hukumomin tsaron sun yi aiki ne da alakar dake tsakaninsa da shugabannin kungiyar inda aka ce zai karba wasu miliyoyin daloli domin tallafawa kungiyar.

Ya yanke shawarar zuwa karbar kudin da kansa saboda tsabar yawansu. Kanu ya rufewa na kusa dashi domin bai sanar musu da abinda ke faruwa ba, kamar yadda majiyoyin tsaro suka ce.

A cikin kwanakin nan, Kanu ya kasance cikin rikicin kudi tare da wasu manyan mukarrabansa.

Bayan isarsa inda zai karba kudin tallafin, jami'an tsaron kasar tare da 'yan sandan kasa da kasa sun damke shi sannan suka dawo da shi Najeriya, majiyar ta tabbatar.

Wannan ne ya kawo karshen guje-guje da boye-boye da Nnamdi Kanu ya dinga tun bayan da ya bar kasar Najeriya. Za a cigaba da shari'arsa a ranar 26 ga watan Yuli.

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, ya zagi jam'iyyarsa kan barazanar da take na maka Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a gaban kotu kan sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC.

Fani-Kayode a jerin wallafar da ya dinga a shafinsa na Twitter, ya soki barazanar da ake wa Matawalle inda ya shawarci jam'iyyarsa da ta dage wurin janyo hankali, Daily Nigerian ta ruwaito.

"Barazanar da PDP ke yi na kai Bello Matawalle kotu a kan komawa jam'iyyar APC ta rashin hankali ce."

Asali: Legit.ng

Online view pixel