Kallon kitse ake yi wa rogo: Bidiyon cikin wata ƴar bukka da ke dauke da katon gado da kayan alatu

Kallon kitse ake yi wa rogo: Bidiyon cikin wata ƴar bukka da ke dauke da katon gado da kayan alatu

  • Bullar wani bidiyo wanda ya nuna alatun da aka sanya a cikin daƙin wata ƴar bukka, ya tabbatar da karin maganar nan ‘sai an gwada akan san na ƙwarai
  • A cikin bidiyon da aka wallafa a Instagram, an kawata kusurwa guda na bukkar da kwanuka sannan a tsakiyar akwai babban gado dauke da shimfida
  • Salon yadda aka shirya bukkar ya sa mutane tofa albarkacin bakunan su a shafukan soshiyal midiya saboda kayan aikin zamani da ake gani a ciki

‘Yan Najeriya sun yi martani ga wani bidiyo da ke yawo a shafukan soshiyal midiya na cikin kuryar dakin wata ƴar bukka.

Bukka ita ce matsugunin da mutane ke amfani da ita a zamanin da amma har yanzu ana samun su a wasu yankuna na karkara.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: PDP ta sake rashi na wasu sanatoci 3, sun koma APC

Kallon kitse ake yi wa rogo: Bidiyon cikin wata ƴar bukka da ke dauke da katon gado da kayan alatu
Yadda aka kawata bukkar ya birge mutane da dama Hoto: @ije-luv
Asali: Instagram

Ana gina ta da gayen dabino. A cikin wani bidiyo da shafin @ije-luv ya wallafa a Instagram, wata baiwar Allah ta nuna cikin kuryar bukkarta wacce ke dauke da kayan aiki na zamani a ciki.

A gefen hagu na bukkar akwai kwanukan samira waɗanda aka jera su da kyau kamar katanga sannan kuma a tsakiyar akwai babban gado da shimfida mai kaloli daban-daban da kuma kayan ɗaki.

KU KARANTA KUMA: 'Karin bayani: Bayan harbe ɗan majalisar Zamfara, an yi garkuwa da ɗansa da direbansa

Mutane sun yi martani daban-daban kan bidiyon

Masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun nuna mamakinsu ga abunda idanunsu ya gani. Wasu sun ce bukkar tayi tsaf fiye da wasu gine-ginen bulo.

@el_hazz ya rubuta:

"Cikakken misali na fankan fankan bat a kilishi.”

@lilianifeomaobayemi ta ce:

"Na taba ganin wannan a baya. A lokacin da nake karama, dakin mutumin da ke gadina ya kasance kamar haka lokacin da ya auri kyakkyawar Bafulatana."

@nne_kaimaa ta yi martani:

"Ma shaa Allah kuma wasu mutanen da ke zaune a cikin manyan gidaje ba sa ma iya tsabtace shi."

A wani labarin, wani fursuna da aka saki kwanan nan daga cibiyar gyara hali ta Katsina, Malam Gambo Mohammed, ya ba da labarin yadda ya kwashe shekaru 21 a gidan yari, yana mai cewa rayuwa ta fi masa a kurkuku fiye da lokacin da ya samu ‘yanci.

A wata hira ta musamman da jaridar Daily Trust, Mohammed ya ce ya girma ne a unguwar PRP Brigade da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Legit.ng ta tattaro cewa ya ce bayan Kammala karatunsa na sakandare, bai iya ci gaba da karatunsa ba, ya kara da cewa ya shiga kasuwancin kifi ne a yankin Galadima na Kasuwar Sabon Gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng