'Karin bayani: Bayan harbe ɗan majalisar Zamfara, an yi garkuwa da ɗansa da direbansa
- Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe dan majalisar jihar Zamfara Mohammed Ahmed
- Yan bindigan sun kashe shi ne a ranar talata a hanyarsa ta zuwa Kano domin ya kai dansa asibiti
- Har wa yau, yan bindigan sun yi awon gaba da dansa da direban motarsa bayan sun kashe shi
Yan bindiga sun harbe dan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar Shinkafi, Mohammed Ahmed har lahira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Rahotanni sun ce yan bindigan sun kashe Ahmed ne a kan hanyar Sheme zuwa Funtua, wani gari da ke kan iyakar jihar Zamfara da Katsina.
DUBA WANNAN: Ango ya fasa aure saboda abinci, ya kuma auri wata a ranar bikin
Zamfara da Katsina, jihohin da ke makwabtaka da juna a Arewa maso Yamma na cikin wuraren da yan bindiga suka addaba da hare-hare.
A halin yanzu ba a gama bayyana cikaken yadda dan majalisar ya rasu ba amma Saidu Anka, magatakarda a Majalisar dokokin jihar Zamfara ya tabbatar da lamarin a cewar Daily Trust.
An kashe Ahmed ne jim kadan bayan manyan yan siyasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar sun sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC) tare da Gwamna Bello Matawalle.
Yan bindigan da suka kashe Mohammed Ahmed sunyi garkuwa da dansa da direbansa
Direktan Watsa Labarai da Hulda da Jama'a na majalisar dokokin jiharzamfara, Malam Mustafa Ja'afaru Kaura shima ya tabbatarwa manema labarai kashe dan majalisar na Zamfara.
KU KARANTA: Nnamdi Kanu na samun goyon bayan dillalan makamai na ƙasashen waje, Dattawan Arewa
Jafaru Kaura ya kuma ce yan bindigan sun yi garkuwa da direban dan majalisar da dansa kamar yadda News Wire ta ruwaito.
"Ahmad zai kai dansa asibiti ne a jihar Kano.
"Yan bindigan sun yi garkuwa da direba da dan dan majalisar," a cewar Jafaru-Kaura.
Mafarauta sun ɗirkawa mai garkuwa harsashi ya mutu wurin karɓar kuɗin fansa
A wani rahoton daban, mafarauta sun harbe wani mutum da ke cikin gungun masu garkuwa da mutane uku har lahira yayin da ya tafi karbar kudin fansa a kauyen Abobo a karamar hukumar Okehi na jihar Kogi, Daily Trust ta ruwaito.
Wani mafarauci da ke cikin wadanda suka shirya atisayen, ya ce an yi harbin ne misalin karfe 5.23 na asubahi a ranar Talata.
Mutumin ya fito ne daga wurin da ya ke boye a yankin Abobo, bayan Itakpe, wasu yan kilomita kadan daga babban titi.
Asali: Legit.ng