Da Ɗuminsa: FG Ta Faɗi Ranar da Zata Kulle Layukan Wayar da Ba'a Haɗasu da NIN Ba

Da Ɗuminsa: FG Ta Faɗi Ranar da Zata Kulle Layukan Wayar da Ba'a Haɗasu da NIN Ba

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar da zata fara kulle duk wani layin waya da ba'a haɗa shi da lambar zama ɗan ƙasa NIN ba
  • Gwamnatin ta faɗi haka ne a wani jawabi da hukumar sadarwa NCC tare da hukumar NIMC suka fitar
  • Ministan sadarwa, Isa Pantami, a madadin FG ya yaba da biyayyar da yan Najeriya suka nunawa umarnin haɗa NIN-SIM

Gwamnatin tarayya ta amince da ƙara wa'adin haɗa layin waya da lambar katin ɗan kasa NIN (SIM-NIN) zuwa 26 ga watan Yuli, 2021, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Gwamnatin tace ta ɗauki wannan matakin ne bayan wasu masu faɗa a ji sun bata shawarar ya kamata ta sake yin nazari a kan aikin haɗa NIN-SIM.

KARANTA ANAN: Wani Tsohon Kwamishina Ya Sha da Ƙyar Yayin da Yan Bindiga Suka Buɗe Wa Tawagar Motocinsa Wuta

Ta ƙara da cewa an samu wannan cigaban ne biyo bayan ƙarin adadin yan Najeriya dake shiga tsarin a faɗin ƙasar nan.

FG ta ƙara wa'adin haɗa NIN da SIM
Da Ɗuminsa: FG Ta Faɗi Ranar da Zata Kulle Layukan Wayar da Ba'a Haɗasu da NIN Ba Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Gwamnatin ta sanarda haka ne a wani jawabi da kakakin hukumar sadarwa (NCC), Dr. Ikechukwu Adinde, da kuma takwaransa na hukumar samar da katin zama ɗan ƙasa (NIMC), Mr Kayode Adegoke, suka sanya wa hannu.

Wani ɓangaren jawabin yace:

"Gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin wa'adin haɗa layin waya da lambar NIN a ƙoƙarin da take na baiwa yan ƙasa damar mallakar NIN, kuma yana da matuƙar amfani mutane su yi amfani da damar wannan ƙarin lokacin."

"A halin yanzun yan Najeriya miliyan 57.3m ne suka mallaki lambar NIN, da ƙiyasin haɗa lambar da layuka 3-4."

"Kasancewar an ƙara yawan cibiyoyin rijistar katin ɗan ƙasa a faɗin ƙasa, kowane mutum mai kishin ƙasarsa yana da damar mallakar NIN cikin sauƙi.

Pantami ya yaba da hakurin yan Najeriya

Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami, a madadin gwamnatin tarayya ya yaba da haƙurin yan Najeriya da kuma halin dattako da biyayyar da suka yiwa umarnin gwamnati na haɗa SIM-NIN.

KARANTA ANAN: Bayan Matawalle, Jam'iyyar PDP Ta Faɗi Babban Dalilin da Yasa Gwamnoni Ke Ficewa Daga Cikinta

Shugaban hukumar NCC, Prof Umar Garba Dambatta, tare da takwaransa na NIMC, Engr Aliyu Azeez, sun roƙi yan Najeriya da su yi amfani da wannan damar su mallaki NIN, sannan su haɗata da layin wayarsu.

Jawabin yace: "Ministan sadarwa, Isa Pantami, a madadin FG, ya yaba da biyayyar da yan Najeriya suka yi wa umarnin gwamnati na haɗa NIN-SIM."

A wani labarin kuma Wata Sabuwa, Obasanjo Ya Sake Yin Magana a Kan Jita-Jitar An Sauya Buhari da Jibrin Sudan

Obasanjo ya sake maganan kan jita-jitar da aka yi a baya lokacin da Buhari ya daɗe a Landan neman Lafiya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Tsohon shugaban yace wannan rahoton da aka yaɗa a wancan lokacin babban abun dariya ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262