Bayan yara 6, mata ta sake haifan ‘yan 4 a lokaci guda, mijin na neman agaji
- Wasu ma'aurata a Benin wadanda ke da yara shida sun roki 'yan Najeriya da su kawo musu dauki bayan sun sake haifan wasu yara hudu a lokaci guda
- Mijin mai suna Austin Ohenhen ya ce ya firgita lokacin da ya ji labarin cewa matar sa ta haifi 'yan hudu
- Mutumin ya yi ta maza ya dawo gida ne kawai bayan kalmomin ƙarfafa gwiwa daga abokai da dangi
- A nata bangaren, sabuwar uwar ta roki da a taimaka mata, tana mai cewa ita da mijinta a yanzu duk ba su da aikin yi
Wasu ma'aurata a Benin, babban birnin jihar Edo, sun samu kyautar 'yan hudu bayan ‘ya'ya shida da suka Haifa a baya.
Da yake magana da Legit TV, mijin mai suna Austin Ohenhen ya ce ya gudu na wani dan lokaci bayan ya ji labarin.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: Ƴan bindiga sun bindige ɗan majalisar jihar Zamfara har lahira
A cewar Austin, ya koma gida ne bayan kalmomin ƙarfafa gwiwa da ya samu daga abokai da dangi.
Ita ma da take magana, sabuwar mahaifiyar ta ce lokacin da take da ciki, ta yi tunanin zubar da cikin amma babu kudin da za a yi hakan.
Matar mai kimanin shekaru 35 a duniya mai ‘ya’ya goma ta ce tun zuwan ‘yan hudun, Allah na ta budawa iyalin.
Ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su kawo musu dauki domin ita da mijinta a halin yanzu ba su da aikin yi kuma suna bukatar taimako wajen kula da jariran.
KU KARANTA KUMA: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Osun, babu asarar rai
A cewar sabuwar uwar, ta auri mijinta a shekarar 2005 kuma sun tsara haihuwar yara hudu.
A wani labarin, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce karuwar yawan mutane a Najeriya na iya zama matsala idan ba a sarrafa hakan da kyau ba, The Cable ta ruwaito.
Tsohon shugaban kasar ya yi wannan gargadin ne yayin da yake magana a wani taro a jihar Ogun ranar Lahadi.
A farkon wannan watan, Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto wanda ya kiyasta cewa yawan mutanen Najeriya ya haura miliyan 211.
Asali: Legit.ng