Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Osun, babu asarar rai
- An samu rashin jituwa tsakanin yan kasuwa Hausawa da Yarbawa a Osun
- Rikici yayi sanadiyar jikkatan wasu cikin bangarorin biyu
- An kai kara wajen Sarkin Owode domin sulhu
Hankali ya tashi a Owode-Ede, karamar hukumar Ede North ta jihar Osun ranar Talata yayinda rikici ya barke tsakanin matasan Yarbawa da Hausawa masu sayar da kayan miya.
An samu labarin cewa rikici ya auku ne a shararriyar kasuwar Owode.
CityMirrorNews ta ruwaito cewa rikici ya fara ne lokacin da aka umurci wani Bahaushe da ya kasa kayan miyansa a gaban gidan wani mutumi dake cikin kasuwan ya kwashe kayansa.
Shi kuma mai gidan sai ya yi watsi da kayan miyan domin budewa kansa hanya na shiga gidansa.
Kawai sai Bahaushen ya fasa gilashin motar mutumin, bisa rahoton da aka tattaro.
DUBA NAN: Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilim
DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa yan kasuwan Hausawa sun saba kasa kayayyakinsu gaban shaguna da gidajen mutane ba tare da izini ba.
"Wasu sai su kasa kayansu gaban shagon mutum, yayinda wasu zasu kasa a kan gadar shiga," mai idon shaida yace.
Daga karshe an garzaya da Hausawan fadar Sarkin Owode yayinda aka garzaya da wadanda suka jigata asibiti.
Da yiwuwan an fasa zanga-zangan Igboho
A bangare guda, Dan gwagwarmayar Yarbawa, Mr Sunday Adeyemo Igboho, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya karyata labarin dage taron gangamin da ya shirya a Lagos ya kuma roki rundunar yan sanda ta basu kariya, Daily Trust ta ruwaito.
Ana cikin fargaba a gaba daya jihar sakamakon gangamin.
Da safiyar Laraba, an samu rahoton dage gangamin har sai baba ta gani kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng